Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari, ya bayyana cewa yin watsi da harkar ma’adinai ya taimaka ƙwarai wajen ruruta matsalar tsaro da kiraye-kirayen tayar da ƙayar baya a ƙasar nan.
Masari ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai wa Ministan Ma’adinai da Ƙarara, Olamilekan Adegbite a ofishin sa da ke Abuja.
A ziyarar wadda Masari ya kai ranar Litinin, ya ce masu ƙarajin tayar da ƙayar bayan neman wani haƙƙin su na albarkatun za su yi gum da bakin su matsawar aka maida hankali ana cin moriyar sauran albarkatun ƙasa da ma’adinan da ke sauran sassan Najeriya.
Ya ce matasa sun maida hankali wajen tafka ayyukan laifuka a cikin ƙasa saboda Najeriya ta ƙi maida hankali wajen bunƙasa sauran albarkatun ƙasa, sai ta maida hankali ga fetur kaɗai.
Masari ya ce idan aka maida himma aka bunƙasa sauran fannonin haƙo ma’adinai da albarkatun ƙasa, matasa za su ƙara samun ayyukan yi sosai.
Cikin jawabin wanda Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Masari, Audu Labaran ya fitar ga manema labarai, ya ce idan aka yi hakan, za a samu ragowar matasa masu aikata muggan laifuka sosai.
Daga nan ya nemi haɗin kan Ministan Ma’adinai da Ƙarafa ya haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Katsina domin a ci moriyar albarkatun ƙasa da ma’adinan da ke kwance a cikin Jihar Katsina.
CIkin makon jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Gwamna Masari na cewa, babu ranar da ‘yan bindiga ba su jidar mutane a Ƙananan Hukumomi 10.
Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya bayyana cewa a cikin Ƙananan Hukumomi 34 na jihar Katsina, jihohi 10 na fama da farmakin mahara masu garkuwa da mutane da satar dukiyoyi, a kowace rana.
Masari ya shaida wa Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Faruk Yahaya haka, a lokacin da ya kai masa jiyara a Katsina, ranar Alhamis.
Ya shaida masa cewa ‘yan bindiga su addabi ƙananan hukumomi 10 su na kisa, fyade, garkuwa da mutane, illatarwa, banka wa gidaje wuta da satar shanu.
Gwamna ya ce Gwamnatin Katsina ba ta gamsu da yanayin matsalar tsaron da ta dabaibaye jihar Katsina, tare da ya zama tilas a kawo ƙarshen lamarin.
“Mu na bukatar a samar da zaman lafiya cikin hanzari, domin sojoji su koma barikin su, su bar ‘yan, su kuma ‘yan sanda su karɓi aikin tsaron a hannun su.
Sannan kuma ya jaddada wa Shugaban Sojoji cewa Gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa sojojin Najeriya goyon baya, yadda za a kawar da matsalar tsaro.
A na sa jawabin, Janar Faruk ya shaida cewa ya kai ziyara Jihar Katsina domin ganawa da Sojojin Najeriya masu aikin tsaro a jihar domin ya gana dasu kuma ya ji daga bakin su halin da su ke ciki.
Daga cikin Ƙananan Hukumomi 10 da ‘yan bindiga su ke kai hare-hare, akwai Batsari, Jibiya, Sabuwa, Faskari, Safana da Ƙanƙara.
Discussion about this post