‘Yan siyasa ke ruruta wutar hare-hare da sace-sacen mutane a Zamfara – Matawalle

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke ruruta wutar rashin tsaro da ake fama da shi a jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana haka jawabi da yayi wa ‘yan jihar ranar Laraba.

” Sai da muka samu saukin hare-hare na ‘yan bindiga na wata tara a jihar mu, wasu ‘yan bindigan da yawa sun ajiye makamai sun rungumi sulhu. Amma kuma wasu ‘yan siyasa da suka ga muna samun nasara sai suka fara yi mana zagon kasa, suka lalata abin.

Sannan kuma gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma, suma ba su mara mana baya ba. Mun shirya ayi sulhu tsakanin jihohi da ‘yan bindiga amma gwamnoni wasu jihohin sun ki. Wannan yana daga cikin dalilin da ya sa hare-haren yayi muni da tsananin gaske a ajihar.

Jihar Zamfara ta fada cikin mummunar yanayi a cikin watannin nan inda hare-haren yan bindiga ya tsananta matuka.

Wannan tashin hankali ba a jihar Zamfara kawai yayi tsanani ba, jihohin Kaduna da Katsina na daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan bindiga yayi tsanani.

Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta biya ‘yan bindiga ko sisi ba idan suka bukaci haka daga jihar.

Har yanzu akwai dalibai na wata makaranta da ‘yan bindiga suka sace a hannun su.

Share.

game da Author