YAJIN AIKIN LIKITOCI: Jangwangwama 10 Da Gwamnati Ta Jefa Talakawan Najeriya

0

Zuwa ranar Litinin ɗin nan dai an share wata ɗaya cur likitocin Najeriya waɗanda ke ƙarƙashin Ƙungiyar NARD, wato Ƙwararrun Likitocin Gwaji na yajin aiki, saboda kasa cimma daidaiton da su ka yi da Gwamnatin Tarayya.

Likitocin NARD sun zargi Gwamnatin Tarayya da ƙin cika masu alƙawurran da ta ɗauka na biyan su haƙƙoƙin su. Tun dai cikin watan Mayu, 2021 Gwamnantin Tarayya ta ɗauki alƙawurran a rubuce, amma har yau ba ta cika ba.

Duk da a kullum sai gwamnati ta yi masu barazanar janye biyan su albashi idan ba su koma bakin aiki ba, har yau ko gezau likitocin ba su yi ba.

Wannan abin takaici da ke faruwa a Najeriya, ƙasar da ta fi sauran ƙasashe ƙarfin arziki a Afrika, ya zo daidai lokacin da cutar kwalara ta ke ci gaba da kashe ɗaruruwan marasa galihun da yanzu haka ƙididdiga ta nuna cutar ta amai da gudawa ta kashe mutum sama da dubu ɗaya a cikin watanni biyu ko uku.

Haka nan kuma iska ya iske kaba na rawa. Ana cikin wannan yajin aiki kuma likitoci daga Najeriya ke ta kwarara zuwa ƙasar Saudiyya, a wani gagarimin shelar neman ƙwararrun likitoci da ƙasar wadda ta fi Najeriya ƙarfin arzikin man fetur ta yi.

Kwaɗayin albashi mai yawa, kusan nunki takwas fiye da na Najeriya, sai kuma ingantattun kayan aiki ya sa likitocin sheƙawa ƙasar Saudiyya aikin likitanci.

Ko shakka babu wannan matsala ta gurgunta fannin kiwon lafiyar Najeriya baki ɗaya.

Saura da me, abin tambaya shi ne su wa wannan matsala za ta fi shafa? Su wa aka jefa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi? Su wa ke iya hawa jirgi su lula Ingila neman magani daga Najeriya? Ya makomar talakan Najeriya za ta kasance a wannan yanayi idan ya tsure da amai da gudawa?

1. Talaka ba shi da zaɓi a wannan yanayi na yajin aikin likitoci. Babu kuɗin magani, babu likitoci, damar samun tallafin magani.

2. Yajin aikin likitoci ba zai shafi lafiyar Shugaban Ƙasa ba. Idan ya ga dama ko susar kunne mai ƙaiƙayi zai iya zuwa Landan a yi masa ya dawo.

3. Talaka ne zai jigata ya tagayyara saboda yajin aikin likitoci. Tun daga Ɗan Majalisar Tarayya, Sanata, Minista, Gwamna, Shugaban Ƙasa da dukkan iyalan su, ba wanda ba zai iya fita wajen Najeriya neman magani ba.

4. Yanayin nan na amai da gudawa kafin layin ganin likita ya zo kan mai cutar kwalara, ya gama jigatar da masu jiyya sun fidda rai, sai dai neman motar gawa, makara da likafani.

5. Babu mafita ga marasa galihu a wanann yajin aiki, sai dai shan magungunan ‘daftan’, marasa ingancin da ake sha a ƙarasa rafkewa maimakon a samu sauƙi.

6. Rige-rigen tafiyar likitocin Najeriya zuwa Saudiyya zai ƙara kusantar da talakawa marasa galihu tururuwa wurin ‘daftocin’ kasuwannin ƙauye, masu sayar da ƙullin garin magnin naira 50, mai ‘warkar’ da cututtuka 50 a cikin minti 50.

7. Talaka zai ƙara uku dalilin dogon zangon yakin aikin likitoci. Ga cutar amai da gudawa, ga rashin kuɗin sayen magani. Ga rashin magunguna a asibitocin gwamnati. Ga matsalar ‘yan bindigar da ko mai tsohon ciki ba su jin nauyin ɗaukewa, ballantana maras lafiyar da su ka san idan sun ɗauke, za a iya sayar da gonar sa a biya su kuɗin fansa.

8. Da gwamnati ta damu da halin ƙuncin da talaka ke ciki, tuni da ta cika wa likitocin alƙawarin da ta ɗaukar masu. Mai ɗaukar albashi ba zai taɓa yarda a ce babu kuɗi ba, alhali a duk ƙarshen wata Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi na raba naira biliyan 600 zuwa 700 a tsakanin su.

9. A wannan yanayin idan cutar korona ta darkako cikin rukunin talakawa, to kakkaɓar-‘ya’yan-kaɗanya za ta riƙa yi. Ba shi dai da kuɗin zuwa asibiti, ko ya je akwai ƙarancin likitocin da za su duba shi har a gano ciwon da ke damun sa.

10. Kafin allurar rigakafin korona ta yi wadatar isa ga talakawa za a ɗauki tsawon lokaci. Kafin sannan matsalar yajin aiki ta kassara su. Cutar amai da gudawa makad da su kwance jaɓe-jaɓe a cibiyoyin sha-ka-tafi, inda jami’an kiwon lafiya ke shanya su a ƙarƙashin inuwar bishiyoyi ana rataya masu ruwa, kafin Allah ya kawo sauƙi ko kuma rai ya yi halin sa.

Dama Gambo mai waƙa tun cikin 1981 ya fassara irin wannan yanayi:

“Sai a ɗebi ruwan banza da wohi,
A sha ka basilla babu tausai,
A ce yi ta lunda kak ka damu,
Ba warkewa za ka yi ba,
Don Allah lundat ta mi ta?”

Share.

game da Author