Yadda wani mai aikin gidan siyar da abinci ya rika sace fiffike da ƙundun kaji har na naira miliyan 1.2

0

A ranar Juma’a ne kotun majistare dake Iyaganku jihar Oyo ta gurfanar da wasu matasa biyu da da laifin sace fiffike da kundun kaza.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta kama Precious Kumzak mai shekara 30 da Gbadamosi Idris mai shekara 32 da laifin sata, karban kayan sata da hada baki domin ayi sata.

Dan sandan da ya shigar da kara Salewa Ahmed ya bayyana cewa Precious shine baron da yake satar kaya daga shagon da yake aiki yana siyar wa abokinsa Idris.

Ahmed ya ce Precious ya yi aiki kantin cin abinci na ‘Stone Cafe Bar’ dake layin Ring road a Ibadan daga watan Janairu zuwa Yuli 2021.

Ya ce banda fiffike da kundun kaji da yake arcewa da su, Precious ya rika sace dodon kodi da shinkafa daga shagon yana siyar wa abokinsa Idris.

“A lissafe dai kayan shagon da Precious ya rika sacewa sun kan na naira miliyan 1.2.

Ahmed ya ce Satan da Precious ya yi ya saba wa tsarin dokan ‘Criminal Code’ sashen 390 sakin layi na 9, sashin 427 da 516 ta shekarar 2000 na jihar Oyo.

Alkalin kotun Mrs Patricia Adetuyibi ta ce kowannen su, Precious da Idris za su biya belin Naira 500,000 sannan su gabatar da shaida Kuma
Za a cigaba da shari’a ranar 6 ga Oktoba.

Share.

game da Author