Shugaban Cocin Household of God Church, Chris Okotie, ya bayyana cewa marigayi fasto TB Joshua, ya rika damfarar mabiyan sa inda yake kwatanta kansa da Annabi Isa, wato Jesus.
Okotie ya ce ya daɗe yan ayi wa mutane bayanin cewa su nesanta kansu da marigayi TB Joshua domin bokanci da siddabaru yake yi wa mabiyan sa suke ganin kaman wani annabi ne kamar yadda yake kiran kan sa.
” Joshua ya rika kiran kansa annabi inda yake haɗa kansa da Annabi Isa, wato Jesus.
A baya Okotie ya taba cewa TB Joshua tantirin Boka ne dake damfaran mabiyan sa.
Okotie ya ce ba tun yanzu ba ya ke ja wa mabiyan sa kunne cewa su guje wannan Coci domin ba bu gaskiya a cikin abinda cocin ke yi ƙarƙashin Joshua.
” Ba ya kiran kansa Mai wa’azi ko limami, gaba daya yana kiran kansa annabi ne, a ina ko ake yin haka, shi shi.
Okotie ya saka wani bidiyo mai tsawon mintuna 72 a shafin sa ta facebook inda ya yi kaca-kaca da marigayin.
Shi dai TB Joshua, ba a Najeriya ba har daga ƙasashen waje wato ƙasashen duniya ana yi tattaki zuwa Cocin sa da ke jihar Legas.
Ko da aka sanar da rasuwar sa, mabiyan sa da dama sun riƙa musanta rasuwar na sa cewa annabi baya mutuwa domin shi annabi ne.
Tuni dai an birne marigayin a Legas a cikin watan Mayu.