Shugaban Hukumar raya koguna na Hadejia-Jama’re Ma’amun Da’u-Aliyu, ya bayyana cewa hukumar ta dukufa wajen shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da yake jawo asarar rayuka da dokiyoyin al’ummar dake zaune a yankin Kano, Jigawa da Bauchi.
Da’u-Aliyu wanda ya kama aiki ne a matsayin shugaba a hukumar raya kogunan ta Hadejia-Jama’re a cikin wannan shekara ya sha alwashin magance matsalar ambaliyar ruwa a jahohin gwargwadon ikon da yake da shi.
Ya shaidawa Yan Jarida cewa ba gaskiya bane jita-jita da wasu ke yadawa wai ambaliyar ruwa na faruwa ne sakamakon bude Tiga Dam, Da’u-Aliyu yace ba haka bane, ya ce hukumar sa bata da ikon rufewa da bude Tiga Dam saboda doka ta hana yin hakan.
“Gaskiyar magana ita ce ambaliyar ruwa tana faruwa ne sakamakon ruwan sama mai yawa idan kasa ta shanye ruwa mai yawa sai ruwan sama ya gangara ya koma koguna mafi kusa daga nan shima kogin idan ya cika ya bunkasa sai yayi ambaliya zuwa gunaki da gidajen dake kan hanyar ruwa”.
Da’u-Aliyu ya jaddada cewa Hukumar Hadejia-Jama’re bata bude Tiga Dam saboda akwai doka ta duniya wanda ta haramta yin hakan saboda abarwa al’ummu na kusa da nisa yin amfani da ruwan. Yace Tiga Dam akoda yaushe cikin rani da damuna tana bude saboda dokar duniya ce ta nuna haka.
Tiga Dam tanada ruwa da yakai litre biliyan 1.9 kuma a kullum a bude yake shiyasa ake samun ambaliya cikin damuna saboda ruwa yafi yawa a lokacin damuna.
Kuma abu na biyu dake jawo ambaliya shi ne ciyawar Kachalla dake fitowa a cikin kogunan dake a yankin Hadejia har zuwa tafkin chadi. Ciyawar tana hana ruwa wuchewa kuma ta jawo kogin ya cushe ya rasa hanya daga nan sai yayi ambaliya zuwa gunakai da gidaje.
Kokarin magance marsalar ambaliya
Hukumar ta Hadejia-Jama’re cikin shekaru uku da suka wuce tana kokarin cire ciyawar Kachalla saboda fadada hanyar ruwan. A cikin wannan shekara 2021 gwamnatin tarayya ta ware kudade domin a siyo motoci masu cire Kachalla da ake kira da (Aquatic excavator) motar tana iya aikin cire Kachalla mai yawa a cikin lokaci kadan, inji Da’u-Aliyu
Da izinin Allah zuwa watan October motar ta cire ciyawar Kachalla zata shigo Nageriya domin aikin da kuma fadada girman kogin Hadejia-Jama’re
Bayan haka, hukumar Hadejia-Jama’re tana gina shengi mai nisan kilomita 3.8 a garin Auyo domin kare garin daga ambaliya. A baya sai da ambaliya ta cinye garin Auyo shi yasa muke kokarin magance marsalar faruwar hakan nan gaba, inji Da’u-Aliyu.