Yadda Messi ya ɓarke da kuka a lokacin da ya ke jawabin bankwana a Barcelona

0

Fitaccen ɗan wasan duniya wanda ya fi kowa cin kofin gwanayen ƴan kwallo a duniya, Leo Messi ya bayyana cewa bai ta ɓa saka wa a zuciyar sa cewa zai ga irin wannan rana da zai yi sallama da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ba.

A yayin jawabin sa, Messi ya ɓarke da kuka, har sai da aka ɗan dakata tukunna kafin daga baya ya ci gaba.

” Ban taba tunanin a nan kusa-kusa zan fice daga Barcelona ba, saboda ƙauna da soyayyar da ke ke tsakanina, ba tare da ƙungiyar Barcelona ba kawai, har da mutanen Barcelona.

” Na yi wa matata da ƴaƴa na uku alƙawarin za mu ci gaba da zama a Barcelona, amma kuma hakan yanzu ba zai yiwu ba. Na yi duk abinda zan iyayi don in ci gaba da zama a Barcelona amma hakan bai yiwu ba, haka kuma ita kanta ƙungiyar ita ma ta yi nata ƙoƙarin amma dokokin ƙasar Spain ya sa babu yadda za muyi, Dole mu hakura da juna kowa ya kama gaban sa.

Messi ya kara da cewa, rayuwarsa kaf a Barcelona yayi saboda haka dole ya ji ba daɗi musamman ƴan kallo waɗanda ke nuna masa soyayyar da bashi misiltuwa.

Ana raɗe-raɗin Messi zai koma PSG ne ko kuma wata ƙungiyar. Sai dai har yanzu bai faɗi inda zai nufa ba.

Share.

game da Author