Yadda matasa 11 da basu ci jarabawar shiga aikin soja ba suka rasu a hatsarin rugujewar gada a Jigawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana yadda hadarin motoci biyu suka yi sanadiyyar mutuwar matafiya 21.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Lawan Shisu Adam ya ce rundunar ta samu labarin abin da ya faru bayan kiran gaggawar da aka yi wa ‘yan sandan ranar Lahadi da misalin karfe 6 na safe daga kauyen Rabadi.

Hadarin ya auku ne a hanyar Gwaram inda ‘Hurmmer Bus’ dake dauke da mutum 18 wanda ya yo lodin fasinja daga jihar Kano zuwa Adamawa da mota Tipa dauke da mutum uku suka yi karo suka fada cikin wani kwalbati dake cike da ruwa.

An tsamo gawarwakin mutum 21 daga cikin wannan kwalbati wanda duk likita ya tabbatar sun mutu.

Mutum daya mai suna Simon Chinapi mai shekara 26 ya tsira da ransa a hadarin.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin wadanda suka rasu, akwai wasu daliban da suka je jarabawar neman shiga aikin soja amma kuma basu yi nasara ba da kuma wasu fasinjojin

Rundunar ‘yan sanda ta ce za ta ci gaba da bincike akai.

Share.

game da Author