Yadda Jami’an Kwastan suka kashe mutum biyar saboda buhun shinkafa a Katsina

0

Tarzoma ta ɓarke a garin Jibiya da ke cikin jihar Katsina sanadiyyar kisan mutum biyar da jami’an kwastan su ka yi, lokacin da su ka biyo masu ɗauke da buhunan shinkafar sumogal a sukwane.

Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa motar jami’an kwastan ta ƙwace, inda ya afka cikin mutane ta banke da dama, biyar su ka mutu kuma wasu masu yawa su ka ji raunuka.

“Gaskiya jami’an kwastan ɗin su ma a guje su ke, gudu na fitar hankali. Motar su ta ƙwace ta sake titi ta kashe mutum biyar, wasu da dama su ka ji raunuka.

“Yanzu haka waɗanda su ka ji ciwo su na asibiti. Sai dai hasalallun matasa sun tayar da tarzoma, inda su ka banka wa motar kwastan wuta tare da yi mata rugu-rugu.”

Majiyar ta ce kwastan ɗin sun biyo masu ɗauke da shinkafar sumogal ne, wadda aka shigo da ita daga Jamhuriyar Nijar.

Ba wannan karo na farko ko na biyu da jami’an kwastan ke kashe mutane wurin gudun fanfalaƙin kamo ‘yan sumogal ɗin shinkafa ba.

An nemi jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran’Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, amma wayar da ta ƙi samuwa.

Share.

game da Author