Yadda aka tsinci ɗaliban makarantar Yauri a dajin Ɗansadau suna watangaririya bayan sun arce daga hannun ƴan bindiga

0

Ɗalibai biyu daga cikin ɗaliban makarantar Gwamnatin tarayya dake Yauri Jihar Kebbi sun arce daga hannun ƴan bindiga.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda Ƴan bindiga suka sace ɗalibai da wasu malaman makarantan bayan artabu a ranar 17 ga watan June.

Ɗaliban da suka arce sun haɗa da mace da namiji.

An tsince su ne a daji a yankin Dansadau dake Karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara ranar Asabar.

Mutanen garin Ɗansadau sun shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa an tsinci ɗaliban ne da misalin karfe biyar na yamma a jiya Asabar kuma tuni har an miƙa su ga ƴan Sandan jihar Zamfara, garin Gusau.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara, Hussaini Rabiu ya bayyana wa manema labarai cewa an tsinci ɗaliban a ƙauyen Babbar Doka dake masarautar Ɗan Sadau suna watangaririya.

Rabiu ya ce za a mika ɗaliban ga gwamnatin jihar Kebbi bayan an sallame su daga asibiti.

Ɗaliban da suka arce daga hannun ƴan bindigan sun haɗa da Maryam Abdulkarim, mai shekari 15 ƴar asalin jihar Neja da Farouk Buhari, 17 ɗan jihar Kebbi.

Share.

game da Author