Yadda aka kaure da faɗa tsakanin Ƴan shia da mazauna Ɗorayi Babba a birnin Kano

0

Mazauna unguwar Ɗorayi Babba da ke jihar Kano sun hana ƴan shi’a gudanar da wani taron ƙungiyar da suka yi duk shekara mai suna taron Ghadeer a unguwar.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa rikici ya barke ne bayan ƴan shi’an sun yi gungu a wani filin wani ɗan uwan su domin yin wannan taro.

” Mutanen wannan unguwa sun nemi su siya wannan fili domin ƴan shi an su daina zuwa musu unguwa suna gudanar da tarukan su, amma mai filin ya tsawwala musu kudi. Sun ce hankalin su a unguwar ba ya samun natsuwa idan yan shi a na taro a unguwar.

” Da suka taru a wannan fili domin gudanar da taron sai ko matasan unguwa suka afka musu domin su kora su, daga nan sai aka kaure da faɗa.

An ji wa wasu rauni sannan kakakin ƴan sandan Kano Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wasu mutum hudu.

Share.

game da Author