Hadimin sanata Bala Na’Allah da ke wakiltar Jihar Kebbi a majalisar dattawa, Sanata Bala Ibn Na’Allah, Garba Mohammed ya bayyana cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun bi babban ɗan sanatan Abdulkarim har gida suka kashe shi.
Abdulkarim mazaunin unguwar Malali ne dake Kaduna.
Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana wa manema labarai cewa waɗanda suka kashe Abdulkarim, sun iske shi gida ne suka ɗaɗɗaure shi sannan suka murɗe masa wuya har sai da ya mutu. Sannan kuma suka tafi da motarsa
Jalige ya ce ƴan sanda sun fara bincike akai.
An yi jana’izar Abdulkarim a maƙabartar unguwar sarki dake Kaduna.