Zargi: Ana amfani da wasu hotunan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, inda ya ke tsaye kusa da wani mutumi a Amirka, ana zargin wai yana kasar ne dan amsa tambayoyi dangane da zargin da hukumar FBI ke tuhumarsa da su.
Tsohon shugaban kungiyar leken asirin Sfeto Janar na ‘yan sanda (IGP-IRT) a Najeriya Abba Kyari ya kasance a idon jama’a kwanan nan, abun da ya biyo bayan tuhumar da wata kotu a daya daga cikin gundumomin jihar California ta Amirka ta yi masa, na cewa yana da hannu a zambar dalan Amirka milliyan daya da digo dayan da Ramon Abbas (wanda aka fi sani da Hushpuppi) ya aikata.
Wannan tuhuma ta Kyari na zuwa ne bayan da hukumar FBI ta dauki watanni tana binciken sirri, inda take zargin shi da ma’amala da Abbas sa’annan ta bukaci da a kama shi a tsare na tsawon kwanaki 10 kafin kotun ta fara zama.
Koke-koken jama’ar da ya biyo bayan labarin tuhumar da FBI ke wa fitaccen jami’in dan sandan ya sanya hukumar ‘yan sandan dakatar da shi daga aiki a matsayin san a Kwamishinan ‘yan sanda bisa shawrar Sifeto Janar na ‘yan sandan Mr Usman Baba daga ranar 31 ga watan Yulin 2021.
A yanzu haka Kyari na fiskantar wani kwamitin binciken sa Sifeto Janar din ya kafa a karkashin jagorancin mataimakin shi Joseph Egbunike.
To sai dai akwai labaran da ke yawo a kafofin sadarwar soshiyal mediya wadanda ke zargi wai Kyari ya gabatar da kansa ga jami’an Amirkan. Mutane fiye da 500 suka raba labarin wanda ya samo tushe daga shafin wani mai suna “Jihar Katsina A Yau”
Ranar 2 ga watan Ogosta wani mai amfani da shafin Facebook da suna Jihar Katsina A Yau, ya wallafa wani labarin da ke cewa Kyari yana Amirka yana kokarin wanke kansa daga zarge-zargen da aka yi masa.
Hotunan da aka wallafa na dauke da wasu kalaman da aka rubuta a hausa kamar haka:
“Allah ya zama gatanka, ya kuma tsare mana kai DCP Abba Kyari. Daga Musa Garba Augie.
Sarkin yakin Najeriya DCP Abba Kyari ya sauka a jihar California na kasa Amirla domin kare kansa daga tuhume-tuhumen da ake masa. Allah ka taimake shi ka yi masa kariya daga sharrin dukkan wani abun sharri Ameen. Allah ga bawanka kai kadai za ka iya kare shi daga dukkan sharri. Allah ka yi masa mafita.”
Wannan sako ya janyo tausayi da addu’o’I daga ma’abota shafin tun daga aka wallafa ranar biyu ga watan Ogosta 2021
Tantancewa
Dubawa ta fara da binciken inda hotunan suka fito, daga nan ne ta gano cewa Kyari ne ya wallafa hotunan da kan shi a shafin Facebook a 2019.
A karkashin hotunan ya yi bayani kamar haka: “ziyara zuwa ofishin babban sakataren Amirka a Washington DC a matsayin wani bangare na shirin mu. Duk da kalubale masu dimbin yawan da muke fiskanta, na yi amanar cewa ‘yan Najeriya za su iya habaka kasar mu cikin yaddar Allah,” haka ya rubuta a hotunan da ya wallafa ranar 20 ga watan Afrilun 2019.
A halin yanzu dai Kyari na fiskantar wani kwamiti na musamman da ke masa bincike.
A Karshe
Hotun da ake yadawa cewa Kyari ya tafi Amurka domin ya amsa tuhume-tuhumen da hukumar leken asirin Amurka FBI ke masa karya ne. An dauko hotunan ne daga shafin Kyari na Facebbok.
Discussion about this post