Wani Alƙalin Majistare a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, ya tura Aminu ‘Yar’Adua Kurkukun Yola, bisa tuhumar sa da banke mutum huɗu da mota su ka mutu.
Aminu wanda ɗan tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Shehu ‘Yar’Adua ne, ya na karatu ne a Jami’ar AUN da ke Yola, kotu na hutumar sa da laifin kashe mutum huɗu ta hanyar tuƙin ganganci da mota.
Hatsarin dai ya afku a ranar 23 Ga Yuni, 2021.
Rahoton ‘Yan Sanda masu bincike (FIR), ya nuna nuna mai gabatar da ƙara Sufeto Zakka Musa, ya rubuta cewa, Aminu ya yi tuƙin ganganci a bai-fas ɗin Yola, a ranar 23 Ga Yuni, 2021, inda ya banke mutum shida saboda tsananin gudun da ya ke yi da motar sa.
An shaida wa kotu cewa huɗu daga cikin mutanen da Aminu ya banke sun mutu, sauran biyu kuma sun ji ciwo. Amma su na asibitin Sabon Pegi, a Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu.
“Waɗanda su ka mutu a hatsarin sun haɗa da: A’isha Umar, A’isha Mamadu, Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar.
“Waɗanda su ka samu raunuka, kuma su ke kwance asibiti, sun haɗa da Rejoice Annu da Hajara Aliyu.”
Mai gabatar da ƙara ya ce dangin mamata uku, A’isha Umar, Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar sun nemi a biya su diyyar naira miliyan 15.
Sai dai kuma yayin da aka karnato wa Aminu ‘Yar’Adua tuhumar da ake yi masa, ya ce ƙarya ce, bai aikata laifin ba.
Sai da ta kai dai Mai Gabatar da Ƙara ya roƙi kotu a ɗaya shari’ar domin ya buga kwafen tuhumar ya aika wa Daraktan Shigar da Ƙararraki na Jiha (DPP), domin neman shawara.
Mai Shari’a Jummai Ibrahim ta ɗage ƙara zuwa 19 Ga Agusta, kuma ta tura Aminu Kurkuku.