Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya, masu girma, masu daraja, masu albarka! Kamar yadda kuka sani, dukkanin mu dai muna ji, muna sane, kuma muna ganin irin halin da kasar nan tamu mai albarka ta samu kan ta ciki a yau? Wanda abu ne a fili karara, wanda ba ya bukatar sai an yi ta lissafo matsalolin kasar nan a koda yaushe, sam ina ganin babu bukatar yin hakan, kawai dai abun sani shine, KOWA YA YARDA, KUMA KOWA YA AMINCE CEWA, AKWAI MATSALA A KASAR NAN!
Don haka, abun da kawai zamu ci gaba da yi a halin yanzu shine, kokari, da bayar da gudummawar samar da mafita daga wadannan matsalolin, tare da bin halastaccin hanyoyi, kuma ingantattu, domin samar da mafita, tare kuma da hada wa da yin addu’a da rokon Allah ya kawo muna mafita mai dorewa!
‘Yan uwana masu girma! Zan gaya maku gaskiya, kuma tsakanina da Allah, ba tare da la’akari da wani, ko wasu ba. Kuma zan fadi wannan magana ne, ba tare da wata shakka ko jin tsoron wani ba, kuma ba tare da wata manufa ta cin mutuncin wani ko wasu ba, ko tozarta wani ko wasu ba. Kuma wannan magana da zan fadi, zan fade ta ne, tare da sani na da kuma imanin cewa zan hadu da Allah, zan tsaya gaban Allah, gobe alkiyama, domin in amsa tambayoyi a kan ta. Don haka, wannan magana, bani da wani shakku ko kokwanto a kan ta.
Sannan wannan magana tawa, idan na fade ta, ina sane da cewa, lallai mutane zasu fahimce ta, tare da kokarin fassara ta a iya matsayin fahimtarsu, ko ra’ayinsu, da kuma tunaninsu. Don haka, ba zan taba damuwa da yadda kowa ya fahimce ta ba, ko ya fassara ta. Kawai manufata akan wannan rubutu, wallahi shine kishin kasa ta Najeriya, da kuma kishin al’ummata, da kuma neman yardar Allah mahaliccina kawai, wannan shine!
Ya ku bayin Allah, al’ummar Najeriya! Kamar yadda kuka sani, tsohon shugaban kasar Najeriya, mai girma Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Allah yasa ya gama lafiya, amin), yayi hira da wata fitacciyar jarida a kasar nan, ko gidan talabijin na turanci, mai suna ‘Arise TV’, a inda ya kawo wasu muhimman maganganu da shawarwari masu muhimmanci, masu kyau, wadanda suke cike da ilimi, da hangen nesa; magana ta dattako, wadda lallai idan ‘yan Najeriya suka rike ta, kuma suka yi aiki da ita tsakaninsu da Allah, ba tare da la’akari da wani ra’ayi ba, to ina mai tabbatar maku da cewa, wallahi, Allah Subhanahu wa Ta’ala, zai taimake mu, ya tausaya muna, yasa muna hannu cikin lamurran mu, kasar mu Najeriya ta gyaru, a zauna lafiya, da ikon Allah!
Janar Ibrahim Babangida dai ba jahili ba ne, mutum ne shi mai ilimi da hangen nesa. Shi mutum ne mai cikakken kishin kasar nan da kuma al’ummarta. Shi mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa, domin ci gaban kasar nan da hadewarta wuri guda, da kuma zaman lafiyarta. Yasan ciki da wajen kasar nan. Allah ya fahimtar da shi matsalolin kasar nan. Mutum ne da baka isa ka zage shi, ko ka soke shi ba, sai dai idan kai mahassadi ne, ko kuma wanda baya son ci gaba, wannan kuma babu abunda zamu ce da kai, illa ka je kayi ta hassadarka, kuma Allah ya fi ka!
Kuma ni, ba wai ina nufin Janar Ibrahim Babangida baya da kuskure ko kasawa ba, a’a, ba haka ba ne. Shi mutum ne, dan Adam, kamar kowa, kuma shi ajizi ne; zai iya yin daidai, kuma zai iya yin kuskure a cikin dukkanin lamurransa. Amma dai, duniya tayi shaida akan wannan bawan Allah, cewa daidai din sa da alkhairansa, sun fi kusakurensa yawa. To tun da haka ne, me ya kamata muyi? Sai mu roki Allah ya yafe kusakurensa, daidai din sa kuwa Allah ya biya shi da mafificin sakamako, duniya da lahira.
Ya ku Jama’ah! Janar Ibrahim Babangida yace bai kamata duk mutumin da zai shugabanci kasar nan ba ya kasa wasu siffofi da halaye da dabi’u masu muhimmanci, kuma nagari. Daga cikin wadannan halaye da dabi’u da siffofi na gari, yace duk mutumin da tsufa ya mamaye shi, bashi da karfin da zai jagoranci al’ummah, wato mai yawan shekaru, kuma mutumin da ya haura ko ya wuce shekaru sittin (60) a duniya, to bai dace ya zama shugaban kasar nan ba. Domin irin wannan mutum, babu wani abu da zai iya kullawa kasar nan in ban da shiririta da tanbele da shirme da rashin tabbas.
Wannan ra’ayi na Janar Ibrahim Babangida ai ko addini ma ya tabbatar da shi. Domin ba’a bayar da shugabanci ga mutum mai rauni, ko marar lafiya da sauransu!
Ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya! Wallahi, wallahi, wallahi, babu wanda zai soki Janar Ibrahim Babangida akan wannan magana sai wanda yake wawa, jahili, dakiki, wanda sam bai san me yake yi ba.
Ku sanai, Najeriya kasa ce muhimmiya a gare mu. Bamu da wata kasa da muke so, kuma muke kauna, kamar Najeriya. Bamu da wani wuri, wurin zuwa, kamar Najeriya. Don haka, wallahi, ba zamu taba yin shiru, akan duk wani mutumin da yake so ya cuci kasar nan ba, ko a hada kai da shi, a zalunci kasar mu mai albarka, wato Najeriya. Wannan mutum ko dan kudu ne shi, ko dan arewa ne. Ko musulmi ne ko kirista ko marar addini. Kuma ko wane yare ne shi, ko kabila; wallahi duk wannan bai dame mu ba. Abun da ya dame mu kawai, KASAR MU NAJERIYA, DA MAKOMARTA, DA AL’UMMARTA!
Jama’ah, duk wani mutum da yasan abun da yake yi, kuma yasan meye mulki da shugabanci, to yasan cewa duk mutumin da yake tsoho marar karfi, ko marar lafiya, ya kamata ya hakura, ya huta; su zama iyaye, su zama masu bayar da shawara idan suka ga na kasa da su na neman kaucewa daga hanya, kuma su kame kan su daga neman shugabancin kasar nan!
Ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya, wallahi ya zama dole, kuma wajibi akan duk wani dan Najeriya, mai kishin kasar nan da gaske, kuma tsakaninsa da Allah, musa ido sosai, akan duk wasu mutane, ‘yan cuwa-cuwa, masu kishin aljihunsu, ‘yan 419, wadanda suke kokarin cusa muna ra’ayin cewa dole sai mun goyi bayan wani mutum; kuma duk da cewa, dalilai na ilimi da na hankali, duk sun tabbatar muna da cewa wannan mutum ba ya da cikakkiyar lafiya ko karfin da zai shugabanci kasar nan, sannan kuma ga yawan shekaru! Wadannan mutane ba Allah ne a gabansu ba, ba kasar nan ce a gabansu ba, ba al’ummah ce a gabansu ba! Kawai su matsalarsu, shine me zasu samu kawai. To ya zama dole mu sa ido matuka, akan irin wadannan miyagun mutane, bata-gari, ‘yan jari-hujjah; ‘yan fashin ‘yancin al’ummah, da jin dadinsu, da walwalarsu!
Kuma wallahi, ina mai sake tabbatar maku da cewa, goyon bayan Janar Ibrahim Babangida akan wadannan maganganu da yayi, wajibi ne, dole ne, kuma tilas ne! Sannan duk wani mutum, ko shi waye, kuma ko wace jam’iyyah yake, ko shi dan kudu ne ko dan arewa, musulmi ne ko kirista ne, idan kuka ji yana sukar maganganun wannan bawan Allah, to shi munafuki ne, dan cuwa-cuwa, kuma marar kishin kasar nan ne!
Don haka, mu sani, a halin yanzu, irin halin da wannan kasar take ciki, irin wadannan halaye munana da Allah ya jarabi kasar nan da su, to tabbas, tana bukatar irin mutumin da Janar Ibrahim Babangida ya bayyana muna a cikin jawabansa, da kuma hirarsa mai albarka!
‘Yan uwa na ‘yan Najeriya, wallahi, kar ku sake yarda a sake yaudarar ku da maganar bangare ko jam’iyyah ko addini ko yare; duk wannan yaudara ce, kuma ha’inci ne. Najeriya a halin yanzu tana bukatar jajirtaccen shugaba, mai lafiya, mai karfi a jiki, mai sauraron shawarwarin a’ummah, mai cikakken kishin kasa, mai imani, mai tausayi, mai tsoron Allah, masanin tattalin arziki, wanda kuma ya fahimci kasar nan da matsalolinta, fitacce, wanda kuma aka sani a fadin kasashen duniya!
Kar mu yadda da rudin duk wani munafuki, mai kishin aljihunsa, ba kasarsa da a’ummarta ba!
Kuma mu sani, wallahi duk wanda ya goyi bayan wani mutum daga cikin ‘yan siyasa; kuma yana sane da cewa wannan mutum marar lafiya ne, mai rauni ne, wanda bai da karfin da zai jagoranci kasar nan, to ya sani cewa, YA CUCI AL’UMMAR NAJERIYA, YA YAUDARESU, YACI AMANARSU KUMA YA HA’INCESU, kuma ya san cewa, zai tsaya a gaban Allah gobe alkiyama, domin amsa tambayoyi, akan wannan goyon baya da ya ba wannan mutum mai rauni. Don haka sai mu sake tunani. Kuma yanzu ya rage na mu! Mu sani, kamar yadda akwai rayuwa, to kuma tabbas akwai mutuwa, kuma akwai tsayuwa a gaban Allah, kuma tabbas akwai hisabi!
Daga karshe, ya ku ‘yan siyasar Najeriya! Ku sani, ko wace jam’iyyah kuke ciki, wallahi, al’ummar kasar nan suna bin ku babban bashin tsayar masu da mutum mai lafiya, mai cikakken karfin da zai jagoranci kasar nan, kuma mai cikakken kishin kasar nan; mai imani da tausayi da tsoron Allah, wanda mulkinsa zai zama alkhairi ga kasar nan baki daya, kuma kowa ya amfana da karfin ikon Allah. Amma idan kuka ki jin wannan shawara, kuka bi son zuciyar ku, kuka fifita son abun duniya akan maslahar kasarku, to ku sani, duk zamu mutu, mu tsaya a gaban Allah, da mu da ku, domin amsa tambayoyi a gabansa! Kuma kafin nan, sai kun yi dana-sanin aikin da kuka yi, wallahi tun anan duniya!
Wassalamu alaikum,
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Uvete, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.