TSARO: Gwamnatin Kano ta horas sabbin ‘Yan sandan duba gari 5,594

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnati ta horas da ‘yan sandan duba gari 5,504 domin taimakwa wa gwamnati wajen aikin samar da tsaro a jihar.

Ganduje ya fadi haka ne a taron nada kwamitocin tsaro a masarautar Rano da aka yi a karamar hukumar Doguwa ranar Lahadi.

Kakakin gwamnan Abba Anwar ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini.

Gwanduje ya ce samar da tsaro ya zama dole ganin yadda siyasa ya shigo cikin harkar.

“Gwamnati ta ga mahimmancin jawo hankalin mutane wajen samar da tsaro a jihar wanda a dalilin haka ya sa ta horas da wadannan mutane tare da kafa kwamitin tsaro domin samun goyan bayan gwamnati.

“Mun horas da sabbin ‘yan sandan duba gari 704 da suka kammala horas wa a kwalejin horas da ‘yan sanda dake Kaduna.

“A kowace karamar hukuma gwamnati ta horas da mutum 100 inda hakan ya sa aka samu jimlar mutum 3,600 da za su rika gadin kananan hukumomin jihar.

“Ga manyan birane takwas dake jihar za mu zuba duba gari 150, wanda hakan ya kawo jimlar zuwa 1,200.

Ganduje ya mika godiyarsa ga Ma’aikatar Tsaro ta Jiha (DSS), Sojojin Sama, jami’an Civil Defence (NSCDC), hukumar kula da shige da fice, hukumar kwastam, Gidajen horar da kangararru, sarakunan gargajiya, Hukumar Kula da Haramta Fataucin Mutane (NAPTIP), da Kungiyoyin’yan banga kan mara wa gwamnati baya da suka yi wajen samar da tsaro a jihar.

Share.

game da Author