TSARO: A daina kai harin ramuwar gayya – Gargaɗin gwamnatin Kaduna ga mazauna jihar

0

A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira da yin gargaɗi ga mutane da su daina kai hari ramuwar gayya domin kauce wa ɓarkewar sabuwar tashin hankali a jihar.

Gwamnati ta yi wannan kira ne ganin yadda a sanadiyyar harin ramuwar gayya a ka samu salwantar rayuka da dama a karshen makon jiya.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana haka wata takarda da ya fitar ranar Lahadi.

Aruwan ya ce a sanadiyyar kai wannan harin ramuwar gayya, mutane da dama sun rasu. ” Rokon gwamnati shine mutane su daina yanke hukunci da kansu, su bari jami’an tsaro su bi musu hakki.

“Jami’an tsaro sun ce an kashe wadannan mutane domin rama kisan da aka fara yi a kauyen Ungwan Dooh (Mado).

Share.

game da Author