Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta fidda yara akalla 7,361 da ke fama da tsananin daga cikin 10,953 daga watan Janairu zuwa Yunin 2021 a jihar.
Mataimakin jami’in kula da abinci mai gina jiki na jihar George Adam ya fadi haka a taron zango ta biyu da kwamitin inganta cin abincin dake gina garkuwar jikin yara na jihar ta yi a garin Kaduna ranar Juma’a.
Adam ya ce daga cikin yara 7,361 da suka warke daga ciwon tsananin yunwa a jihar yara 2,730 sun warke a kwatan farko na wannan shekara, sannan aka samu karin yara 4,631 da suka warke a kwata ta biyu duk a wannan shekara.
Tsananin yunwa yayi ajalin yara 31 a jihar.