Saura shekara biyu, wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya kare akan kujerar shugabancin Najeriya. Tun bayan dawowa dimokradiyya a jamhuriya ta hudu, ba a taba kafa gwamnatin had’aka (merger) ba sai a zuwan jam’iyar APC a 2015. A lokuta da dama an yi kokarin yin hakan amma bai yiwu ba sai a lokacin mulkin Buhari.
Jam’iyar had’aka, tana da wahalar sha’ani, saboda mutane ne masu bambance-banbance akan komai su ka yadda su tafi akan manufa daya. A irin wannan tafiyar, kowa yana da bukatarsa wacce ya ke so ta tabbata. Idan kuma bai samu yadda ya ke so ba, tabbas zai iya tunanin tarwatsa tafiyar ta kowacce hanya don ya huce takaici.
A tsarin jam’iyar APC, bayan mutanen Arewacin Najeriya sun gama sai su bawa bangaren kudu. Kamar yadda Senator Rufa’i Sani Hanga ya fada, wanda shi jigo ne a cikin gwagwarmayar tabbatar da jam’iyar APC a 2015. Ba mu sani ba, ko za a cika wannan alkawari.
Gaskiya mun fara ganin wasu gwamnoni irinsu Yahaya Bello daga Arewa suna nuna kwad’ayinsu ga tikitin takarar shugabancin kasar a 2023.
A bangaren jam’iyar adawa ta PDP, su ma suna cikin kalubale, don shi kansa shugabancin jam’iyar yana cikin rudani. Mutanen da su ke bukatar takarar shugaban kasa suna da yawa. Wasu suna cewa sai Atiku, wasu kuma suna ganin Kwankwaso zai fi shi. A yayin da gwamnoni masu kujera su ke muzurai a nasu bangaren.
Harsashe ya nuna cewa, za a iya samun canje-canjen jam’iya a tsakanin yan siyasar APC da PDP. Kuma za a yi siyasa mai wahala a wannan lokacin, saboda zuwan jam’iyar had’aka sabon abu ne a jamhuriya ta hudu. Idan har ba a yi adalci ba, to za a iya samun cin amana da siyasar bangaranci saboda haka kasar ta fara tun farko. Ka karanta littafin “The Best Way To Survive In Nigeria” na M.K Soron Dinki.
Allah ya shiryar da mu.