Ɗan wasan Najeriya wanda ya nuna bajinta a gudun kusa da na karshe a wasan Olimpik dake gudana a yanzu haka ya zo na karshe a gudun karshe na Olimpik da aka yi yau a Tokyo.
Adegoke ya shigo filin gudun da karfin sa yana barazanar zai taɓuka wani abu, sai dai kuma bayan kowa ya hau layi an kimtsa tsaf, kuma alkalin wasa ya hura usir, masu gudu kuma sun falfala sai gogan naka ya dakata ya ja baya yana tsalle-tsalle wai cinyarsa ta makale.
Masu gudu daga wasu kasashen kuwa suka cilla abunsu har suka kai karshe.
A karon farko ɗan kasar Italiya yayi nasara a gudun karshe na mita 100, shine ya ci gwal.
Har yanzu dai Najeriya bata ci komai ba a gasar Olimpiks din da ake yi. Baya ga kora da dakatar da ƴan wasan da aka yi, wadanda suke fafatawa duk na kashin baya suke zama.
Dama dai kuma shine ake sa ran zai samu ko da tagulla ne ya ciyo wa Najeriya sai kuma gashi kafa ta harɗe ma sa