Sun kashe dubbai, babu diyya. Sun maida rayuwar miliyoyin jama’a a sansanonin gudun hijira. Sun kashe dubban jami’an tsaro. Sun maida matan wasu da ‘ya’yan wasu matayen su, duk babu hukunci. Daga baya Gwamnatin Tarayya ta yi sun tuba, ta yafe wa ‘yan Boko Haram 3,000 kuma an roƙi al’ummar da waɗannan tubabbun ‘yan ta’adda su ka kassara cewa su karɓe su, su ci gaba da rayuwa a cikin su.
Haka wannan al’amari ya faru ranar Lahadi a Jihar Barno, inda bayan an yi ja-in-ja, daga baya shugabannin al’umma a jihar su ka amince da roƙon da gwamnati ta yi masu cewa su amince tubabbun ‘yan Boko Haram 3,000 su dawo cikin su, a ci gaba da rayuwa tare.
An ɗauki wannan mataki ne a wani taron masu ruwa da tsaki domin ganin an kawo ƙarshen gagarumar matsalar tsaro a Jihar Barno.
Taron dai Gwamnatin Jihar Barno ta shirya shi, bayan Gwamnatin Tarayya ta yafe wa ‘yan Boko Haram ɗin, kuma an gama yi masu huɗubobi, nasihohi da wankin ƙwaƙwalwar kankare masu aƙidar ta’addanci a ƙwaƙwalen su, abin da gwamnatin tarayya ke kira a Turance da ‘de-radicalization’.
Gwamnatin Jihar Barno ta bayyana cewa aƙalla akwai ‘yan ta’adda 3,000 da su ka ajiye makamai su ka yi saranda ga sojojin Najeriya.
Gwamna Babagana Zulum da ya shugabanci taron, ya bayyana cewa baya ga 3,000 ɗin da su ka yi saranda ga sojojin Najeriya, akwai ma wasu ‘yan Boko Haram ɗin su 900 da su ka yi saranda ga sojojin Kamaru.
Zulum ya ce taron mafitar ya zama tilas ganin yadda dubban ‘yan Boko Haram ke ta tururuwar miƙa wuya.
Shugabannin yankunan jama’a daban-daban sun bayar da shawarwarin yadda za a bi matakan da za a karɓi ‘yan ta’addar bayan an sake su.
An shafe sama da sa’o’i biyar ana tattaunawa, inda a ƙarshe aka fitar da tsare-tsaren sharuɗɗan sake karɓar su cikin al’umma.
Taron dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai, masu riƙe da sarautun gargajiya, jami’an tsaro da kungiyoyi daban-daban.
Waɗanda su ka yi jawabai sun haɗa da ‘yan Majalisar Tarayya, na Jiha, sojoji da sauran wakilan jami’an tsaro.
Sauran waɗanda su ka yi magana sun haɗa da waɗanda Boko Haram su ka kassara rayuwar su ko ta ‘yan uwan su da wakilan Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya.
Sharuɗɗa da shawarwarin da su ka ɗauka dai Kwamishinan Shari’a na Jihar Barno Kaka-Shehu Lawan ne ya sa masu hannu.
Sun nemi Gwamnantin Tarayya ta ɗauki batun tubar ‘yan Boko Haram da kaffa-kaffa, kuma bisa matakan da doka ta tanadar.
Kuma sun nemi a ƙara tantance su sosai, a san kowa da inda ya fito da inda za a maida shi, kuma a san irin abin da ya aikata, gudun kada a riƙa sakin tantagaryar ‘yan ta’adda a cikin al’umma.
Sun yi kira ga al’ummar Jihar Barno su zabura wajen tura yaran su makarantun zamani, ta yadda ba za su riƙa gararamba idan sun taso ba, har a riƙa cusa masu aƙidar ta’addanci.
Taron ya kuma amince a kafa cibiyar yi wa ‘yan ta’adda wankan tsarkake su daga ta’addanci a Jihar Barno.
Mahalarta taron sun roƙi rundunar sojojin Najeriya su ci gaba da hare-haren murƙushe ‘yan ISWAP.
Mahalarta sun nemi a riƙa taron manema labarai akai-akai, domin jama’a su ka jin halin da ake ciki da tubabbun da ke yin saranda, an kuma nemi lallai duk wanda ya yi saranda to ya miƙa wuya tare da makaman da ke hannun sa.
Wani hakimi a wurin taron wanda ya ce a gaban sa ‘yan Boko Haram su ka kashe yayan sa, ya bayyana gaskiyar cewa zai yi wahala idan ya koma gida jama’a su amince da batutuwan da aka tattauna a wurin taron, na karɓar tubabbun.
Ya ce da “wahala mutane su yafe masu ballantana a ce su manta da abin da aka yi masu.”