TATTAUNAWA : Yadda za’a samu zaman lafiya a Zamfara ta hanyar sulhu da Ƴan bindiga – Wazirin Ɗansadau

0

Mustapha Umar basarake ne a Jihar Zamfara, shi ne Wazirin Dansadau a masarautar Dansadau wadda ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Maru. A wannan hira da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA, Mustapha Umar yayi bayanai kan yadda za’a cimma zaman lafiya ta hanyar sulhu da Ƴan bindiga da kuma wasu shawarwari da dama da ya bayar akan harkar tsaro a Jihar Zamfara.

PTH: Yankin Dansadau yayi suna wajen harkar numa da kiwo a Jihar Zamfara, yaya lamarin yake yanzu duba da matsalar yan bindiga?

Waziri : Alhamdullah mun yi suna sosai wajen harkan noma da kiwo, amma mun samu jarabawar shigowar bakin makiyaya shekarun baya wanda yasa mukafi kowa famada matsalar tsaro a jihar Zamfara a yanzu. Kasancewar ita masarautar Dansadau tana kudancin jihar Zamfara kuma muna fama da rashin hanya saboda tun daga Gusau har Dansadau babu wani babban gari irin Dansadau, Kuma gabas munada iyaka da jihar katsina, kudu munyi iyaka jihar kaduna, kudu maso yamma munyi iyaka jihar Niger, yamma munyi iyaka jihar Kebbi.

Wannan yasa muna da fadin kasa sosai hakan ne yaba Fulani makiyaya suka shigo kasar tun a can baya, bamu san hakan na iya faruwa ba, kuma duk inda mukayi iyakar nan babu inda hanyar mota take daga Dansadau zuwa wani wurin, kuma Dansadau ba Karamar hukuma bace muna karkashin Karamar Hukumar Maru ne. Sai anyi tafiyar kilomita dari da hamsin tsakanin mu da Maru. Saboda haka kiranmu ga Gwamnati ta dubamu halinda muke ciki. Muna godiya kwarai da gaske bisaga kulawar Gwamnatin jihar Zamfara amman dai muna son karin kulawar ta musammam neman karin jami’an tsaro na soji da kayan yaki, muna kuma kara jinjinawa sojojin dake cikin kasar Dansadau bisaga jajircewar su ba dare ba rana wurin ganin ansamu tsaro a yankin namu, da kuma abokan aikin su Yan sakai mutanen da sukasa kansu wurin aikin tsaro, kuma muna bukatar sojojin subaiwa matasan namu shawarwari da dabarun yaki na zamani don su kaucewa daukar doka a hannunsu.

Sannan ita Gwamnati tabar sauraren mutanen da suke ikirarin su Yan Dansadau ne amman suna iya shekara batareda sun shigo Dansadau ba har madai da wannan matsalar tsaron tai kamari, sun kwashe iyalan su da Yan uwansu amman sai kajisu ta kafafen yada labarai suna batanci ga Gwamnati ko kuma masarautar Dansadau, mu munanan tareda talakkawan mu cikin garin Dansadau muna neman hanyarda za’a zauna lafiya kowa yaje wajen neman abincin shi, kuma munasa Almajiranmu da Iyayenmu malamai wurin yin Addu’o’in samun zama lafiya don haka Gwamnati ta dubemu mudake cikin wannan gari ba Yan sayasa ba da basuda kowa nasu a Dansadau.

Muna godiya ga Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Mutawalle bisa ga jajircewar shi wurin sulhu da Yan bindiga muna son ko yanzun wadanda akayi sulhu kuma suka amshi sulhu to akara samarda sulhun saboda aikin da sojojin sukayi yayi fa’ida kwarai da gaske amman kwanukanda hukumar sojan Nigeriya tabaiwa yankimu yayi kadan saboda yawan kasarmu da kuma iyaka da mukayi da wasu jahohin.

PTH : Ana sukar gwamnatin Jihar Zamfara saboda shirin ta na yin sulhu da Yan bindiga, a matsayinku na shuwagabannin mafi kusa da jama’a ya kuke ganin sulhu da Yan bindiga wajen kawo zaman lafiya?

Wazirin : kasancewar muna da yawan faɗin kasa sosai munyi iyaka da jahohi da yawa kuma bamu da titin mota ko daya inbanda wanda ya fito Gusau zuwa Dansadau. Wannan abunne yake sa muke neman Gwamnatin jihar Zamfara da ta turomu Jami’an ta muzauna mu gayyato makiyayan muyima kanmu faɗa muja layi abunda ya faru ya wuce mu cigaba al’amurranmu na yau da kullum yadda muke a baya. Saboda yawan dajin mu da iyakar mu da wasu jahohi yasa da jami’an tsaro sun fara aiki sai su kaga sun fatattakesu sai abar aikin azo acema Gwamnati angama dasu amman mu munsan suna nan cikin dazukan dake tsakanin mu da sauran jihohin to kaga tunda matsalar tsaro ta dami ko ina a Arewacin Nigeria.

PTH : me yasa kake ganin sulhu da Yan bindiga shi yafi dacewa a yanzu?

Mu munsan suna cikin kasarmu sosai misali mun hana kauyukan dake kewaye damu su fitar masu da duk wani abun masarufi da man fetur mun hanasu shigowa garin Dansadau babu inda zasu samu abubuwan more rayuwa, wannan shi ne ummul aba’isin da suke shigowa garin Dansadau in sun nemi abinci. Wannan shi kesa suna cewa zasu shigo Dansadau to in munji haka sai ace Yan Sakai subar hanyoyinda suke tarewa don hana fitada abincin, domin su sami abinci, su Yan bindigar suna fadawa mutanen kauyukan cewa indai ba’ayi sulhu ba to zasu cigaba da daukar mutane suna garkuwa dasu, kuma muma hanyarmu daga Gus zuwa Dansadau suna matsa mata da taro wai muma su hanamu samun abubuwan more rayuwa. Wallahi wannan shine gaskiyar magana da ke sa suna barazanar shigowa ko harbin, da daukar mutane.

Irin albarkar noman da ake samu a wannan yankin kuma fiyeda kashi hudu bisa biyar na jihar Zamfara nan ne ake samun abincin da jihar kesamu, Kuma mu bamuda makamai kamar yadda suke dashi, sannan su sunsan gidajen mu ko wane irin lokaci suna iya zuwa har gida suyi abunda sukeso, mu kuma bamu san inda suke ba kaga fada irin wannan wanda kai bakasan gidan mutun ba shi kuma yasan naka to saidai abunda Allah yayi, don haka Gwamnati ta kara dubanmu da Idon basira tabar sauraren mutanen da ke adawa da ita masu amfani da sunan Yan Dansadau ne, tasani mu duka ‘ya’yanta ne sai tayi ta hankuri da masu batanci gareta amman dai ta duba talakawanta mazauna Dansadau, munanan tareda su, su kuma masu fadin abunda ba hakaba ne don suyi batanci ga Gwamnati ko masarautar Dansadau bamu tareda su. Fatanmu samun nasara da zaman lafiya mai dorewa muna kuma baiwa shirye shiryen Gwamnati goyon baya a kullum.

PTH : Wane irin gudunmawa masarautar Dansadau take bayarwa wajen samun zaman lafiya da Yan bindiga ganin cewa ana zargin Yan Sakai da daukar doka a hannu?

Wazirin : Alhamdullah masarautar Dansadau karkashin jagorancin Maimartaba Sarkin kudun Dansadau Alhaji Hussaini Umar, talakawan mu da ke cikin garin Dansadau da kauyukan mu sun sani a kullum masarautar takan kirasu ayi taro kan tsaro kuma maimartaba yana nunawa talakawanshu shi su guji daukar doka a hannunsu, kuma su sa Ido a duk lokacin da suka ga wata bakuwar ajiya to su sanarda jami’an tsaro, kuma maimartaba da umarnin gwamnati yana taro da sarakunan Fulani domin ganin yanda za’a shawo kan matsalar tsaro a yankin. A kullum masarautar Dansadau tana nunawa talakawanta su baiwa shirye shiryen gwamnati goyon baya saboda samarda zaman lfy mai dorewa a yankin. Domin samarda zaman lafiya, masarautar Dansadau tayi ta yin kokarin zama tsakanin manoma da makiyaya don gano matsalolin tsaron da ke addabarmu. Masarautar tana daukar nauyin malamai da almajirai wurin gudanar da Addu’o’in samun zama lfy maidorewa a yankin.

Share.

game da Author