Hussaini Ismail shi ne Alƙalin Kotun Shari’a da aka kama daga garin su, aka nausa cikin Dajin Rugu da shi a Jihar Katsina. A cikin wannan tattaunawar musamman da PREMIUM TIMES, ya shaida wa wakilin mu yadda ya shafe kusan watanni biyu ba wanka ba wanki, sai cin dukan tsiya a hannun ‘yan bindigar da ya ce dukkan su ƙananan yara ne. Sai dai kuma ya bayyana yadda su ka sa ya riƙa koya masu yadda ake yin salloli biyar a rana.
Ga bayanan dai nan dalla-dalla daga bakin sa.
PTH: Ya aka yi har ‘yan bindiga su ka kama ka, su ka tafi da kai?
ALKALI: Wannan ƙaddara dai ta faru wajen ƙarfe 3 na yamma mu na cikin kotu. Sai mu ka hango wasu mutum huɗu a kan babura biyu, kowa saɓe da bindiga. Yayin da su ka nufo mu, kowa ya arce. Ni da wani mu ka nufi ɗaya ƙarar, mu na kici-cikin buɗewa su ka damƙe ni. Dama daga shigar su sun tambayi ina Alƙalin ya ke.
Bayan sun danƙe ni, mutum biyu su ka sa ni a tsakiyar su. Mu ka yi ta nausawa cikin daji, har kusan sa’a biyar.
PT: Kuma babu wanda ya kai ma ka ɗauki?
ALƘALI: Wane ɗauki kuma kowa na ta kan sa, kotu ta fashe kowa ya arce. Har su ka ɗora kan babur, babu wanda ya kai min wani agajin ceto na.
PTH: To ina su ka kai ka?
AlƘALI: Bayan tafiya kamar ta sa’o’i huɗu, sai na fara fahimtar mun shiga dajin Zamfara. Dama kuma ba mu daɗe da barin kotun ba su ka ɗaure min idanu na. Hanyar ba ta da kyau kuma ga ciyayi da hakukuwa da ƙaya. Sau uku mu na tsayawa su na sare haki don mu samu hanyar wucewa.
A ƙarshe dai mu ka kai saman wani falalen dutse, inda mu ka taras da sauran ‘yan bindiga masu yawa. Ba ganin su na ke yi ba, amma dai jin yadda ake ta hayaniya a wurin na san su na da yawa ƙwarai.
PTH: Me su ka fara yi maka lokacin da ku ka isa sansanin su?
PTH: Tun ma kafin mu isa sun ƙwaƙule min aljihu, sun kwashe min naira 40,000 da na karɓa a lokacin a Islamiyyar da na ke koyarwar a matsayin kuɗin yin hidimar Sallah.
To da mu ka isa, wani ya harbe ni da ƙafar sa. Ya ce na tsuguna. Mutum biyar su ka nuna ni da bindiga, ogan su ya ce min ina kuɗi? Na ce masa ai sun kwashe abin da ke aljihu na.
Ya daka min tsawa, ya ce ba waɗancan kuɗaɗen ya ke tambaya ba. Na ce ai ni ƙaramin ma’aikaci ne mai ɗaukar albashi. Daga nan ya fusata ya riƙa duka na da bindiga har sau uku. Ya ce idan ban ba su kuɗi ba, zai kashe ni.
Ɗaya daga cikin su ya ce kada su kashe Ni a lokacin. Su bari sai da safe ido na ganin ido, yadda zan ga irin kisan da za su yi min. Kafin su bari na zauna, ɗaya ya falla min duka da bayan addar sa a baya na daya kuma ya kai min naushi da ƙafa a ciki na.
Ogan su ya ce su buɗe min idanu don na ga irin kisan da za su yi min. Na tsorata sosai. Amma dai na fahimta duk razani su ke yi don na yi saurin haɗa su da waɗanda za su biya kuɗi su fanshe ni.
Cikin dare wani da ke cikin masu tsare da ya ke ce min ya lura ni mutumin kirki ne. Saboda haka na haɗa su da waɗanda za su biya fansa ta, ba ya so ya na ina shan wahala.
PTH: Shin waɗannan ‘yan bindiga manya ne ko ƙananan yara ne?
ALƘALI: Duk ƙananan yara ne da ba su wuce shekaru 18, 19 zuwa 20 ba. Babban su shi ne mai shekaru 27. Kuma dukkan su Fulani ne. Saboda idan ka ji sun yi Hausa, to sai za su yi magana da ni.
Waɗanda ke shekaru 20 zuwa sama ana kiran su karfin. Sun raɗa wa kan su sunayen muƙamai na sojoji. Amma dai kaftin da kwamandoji su ne shugabannin su.
PTH: To ta yaya su ka iya kiran iyalin ka har su ka yi magana da su?
ALƘALI: Lokacin da su ka kama sai ɗayan su ya riƙe waya ta. Da safiya ta yi, sai su ka ɗauki lamba ta su ka kira mata ta. Su a can ba a iya samun MTN, sai dai 9mobile da Airtel kaɗai. To daga nan ita kuma mata ta sai ya haɗa su da mahaifin ta da sauran abokan arziki.
PTH: Me su ka riƙa ba ka ka na ci a tsawon kwanakin da ka yi a hannun su?
ALƘALI: Daga taliya sai wake, wani lokaci kuma da biredi. Shi ma su ke ci kuma ba kullum ba.
PTH: To Sallah ga?
ALƘALI: To su dai ba su ma iya sallar ba, ballantana su rika yi duk da cewa Musulmi ne. Na shafe kwanaki da yawa ina yin Sallah a cikin zuciya ta. Ita ma taimamar a zuci na ke ɗaura ta. Har dai wata rana wani ya lura ina karkaɗa ɗan yatsa a lokacin da na ke yin zaman tahiya. Ya tambaye ni abin da na ke yi, na faɗa masa. Daga nan ya ce min na ci gaba da yin Sallah lafiya ƙalau kamar yadda ake yi, babu wanda zai hana ni.
Abin dariya, shi dai wannan ɗin wata rana sai ya tambaye ni ya na so na koya masa yadda zai riƙa yin Sallah. Saboda kawai su bubbuga goshi ƙasa su ke yi, ba su san yadda ake yin sallar ba ma. A haka na koya masu adadin raka’o’in kowace sallah. Kuma na koya masu karatu addu’o’in da ake yi a lokacin ruku’u da sujada kuma na koya masu yadda ake yin alwala.
Sai na fahimci da yawan su sun ma ƙarara su koya. Da sauran ‘yan bindigar su ka dawo su ka ga yadda abokan su ke yin Sallah, ba kamar yadda su ke yi a da ba, sai su ma su ka ce na koya masu.
A hankali dai na zama malamin Islamiyyar su. Kuma daga nan su ka daina duka na, amma ba su daina tambayar kuɗi ba.
PTH: Me kuma ka fahimta dangane da waɗannan ‘yan bindiga?
ALƘALI: Gaskiya abin da na fahimta, kamar ma ba su ba ne ke amfana da kuɗin. Saboda sau da yawa zan ji su na magana da waɗansu kamar ogogin su, waɗanda ko dai a cikin gari su ke zaune ko kuma a cikin wani daji.
Kuma kusan biyar daga cikin su sun nuna min sun gaji da garkuwar da su ke yi da mutane. Biyu daga cikin su sun ce shanun su aka sace, kuma ba su da wata sana’a ko abinci ko abin dogaro, shi ya sa su ka ɗauki bindiga. Wani kuma ya roƙe Ni na samar masa aiki a cikin birni inda zai riƙa samun ko naira 1000 a rana, zai daina garkuwa da mutane.
Kuma na lura su na tsoron mutuwa. Don ko motsi su ka ji sai su gudu su ɓoye. Sannan kuma duk ranar da su ka fita kai hari, su na tunanin ko koma ko a kashe su.
Sannan kuma wasun su sun faɗa min cewa su sun san idan sun mutu za su sha azaba a lahira.
Na kuma lura tantagaryar jahilai ne. Don ko kiran su aka yi, sai su ba ni yawar na duba na ga sunan mai kiran na su. Kuma ni su ke ba na duba masu sauran kuɗin kiran wayar su ko nawa su ka rage.
PTH: A ƙarshe ya aka yi ka kuɓuta?
ALƘALI: Bayan ‘yan uwa da abokan arziki sun haɗa naira miliyan ɗaya da kyar, an turo wanda ya kawo kuɗin. Shi ma ya ci duka saboda sun ce ya tafi zan biyo shi daga baya. Shi kuma ya ce ba zai tafi ba sai tare da ni. Hakan ya ja masa duka. Washegari cikin dare su ka ɗauko ni a kan babur. Bayan kamar tafiyar awa uku. Su ka ajiye ni, su ka ce na kama na yi tafiya ta.
A haka na riƙa fsgamniyar laluben hanya, har na kai inda zan iya samun mota.