TATTAUNAWA: Kasuwar Dawanau ce ma’aunin gane alamomin tsadar abinci da yunwa nan gaba a Arewa – Shugaban Kasuwan Dawanau, Sani Ƙwa

0

Sani Ƙwa shi ne Shugaban Riƙo na kasuwar sayar da kayan abinci ta Dawanau (Dawanau Commodity Market), wadda ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, a Jihar Kano.

Kamar yadda ya shaida a hira da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA, Sani Kwa ya ce shima ya yarda da hasashen da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta yi cewa nan gaba fiye da mutum miliyan 14 za su fuskanci ƙarancin abinci a Arewa.

PTH: Yanzu da ya ke lokacin damina ce, waɗanne irin amfanin gona aka fi buƙata a Kasuwar Dawanau?

SANI ƘWA: To zan iya ce maka duk wasu kayan gonar da ka sani akwai su. Amma dai a yanzu riɗi aka fi buƙata, duk da dai shi ɗin ma babu shi a wadace. An dai ɗan fara samu kaɗan-kaɗan daga Jihar Taraba. Amma idan lokacin sa ya zo, to fa za ka riƙa ganin ana sauke shi tirela-tirela daga Taraba, sai Yobe, sai Bauchi da sauran jihohi.

Kasuwar kayan abinci ta Dawanau kasuwa da ake kawo kayan abinci irin su farin wake da jan wake, citta, masara, gero, dawa, alkama, shinkafa, gyaɗa, gurjiya da sauran su. Za ka yi mamaki kamar yadda ka ke ganin doya a kasuwar nan, sai ka yi tsammanin ko a Jihar Kano ake noma ta. Kasuwannan nan babu kamar ta a Afrika ta Yamma, ko ma na ce Afrika baki ɗaya.

PTH: Idan kaka ta yi, aƙalla ko akasara ana sauke lodin tireloli nawa a kullum na kayan abinci.

SANI ƘWA: Aƙalla ana sauke tireloli da motar katako 300 ko fiye da haka a kowace rana idan kakar amfanin gona ta zo. Banda ma ƙananan motoci kenan.

Ka lura da wani abu guda. Shi riɗi kashi kusan 100 duk a kasuwar Dawanau ake kawo mana shi ko daga ina aka noma shi a Arewacin ƙasar nan. Daga nan ake gyara shi a riƙa fita da shi ƙasashen ƙetare.

Amma kamar gero, dawa, masara da sauran su, to kamar kashi 50 cikin 100 na wanda aka noma a jihohi ne ake kawowa nan kasuwar Dawanau.

Saboda duk inda aka noma kayan abinci manoma kan ajiye wanda za su ci da wanda su ke sayarwa a garuruwan su ga waɗanda ba manoma ba.

PTH: Kwanan nan Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi hasashen cewa nan gaba kaɗan za a yi fama da ƙarancin abinci a Arewacin Najeriya. Shin ya ka ke kallon wannan hasashe na su?

SANI ƘWA: Wannan maganar gaskiya ce. Ko mu mun sha yin rubuce-rubuce muna gaya wa waɗanda lamarin ke hannun su, wato gwamnati waɗannan matsaloli da alamomin ƙarancin abinci da yunwa nan gaba. Dole sai Gwamnanti ta ƙara tashi tsaye ta tallafi manoma da masu sayar da kayan abinci. Mun san gwamnati na bakin ƙoƙarin ta. Amma akwai buƙatar ta rubanya kuma ta riƙa sa ido, ta yadda idan an bada tallafin noma, ta tabbatar da manoma ake ba tallafin, ba wasu ke karkatar da kuɗaɗen a wani ko wasu harkoki daban ba.

Kusan kashi 80 bisa 100 na tallafin noma da gwamanti ke bayarwa, ba ga manoman asali ya ke tafiya ba. Shi ya sa ake ganin gwamnati na ƙoƙari amma kuma ba a ganin wadatar abincin. Kuma kullum sai ƙara tsada ya ke yi, maimakon a samu sauƙi.

Ƙananan Hukumomi sun san manoma na asali, kuma su na da rekod ɗin su. Amma duk inda ka ji ƙungiyar masu noma kaza-da-ƙaza, to yawanci a nan ake samun matsala. Kuma da yawan waɗanda ake bai wa bashin ba noman su ke yi da kuɗin ba. Sannan kuma akan jefa siyasa a cikin lamarin.

PTH: Mu na kan maganar ƙaranci da tsadar abinci

SANI ƘWA: Ai ban sauka daga kan hanya ba. Mu a kasuwar Dawanau daga inda mu ka gane akwai matsalar ƙarancin abinci, to daga inda aka wayi gari jihohin da fataken mu ke zuwa su sayo abinci su sayar, yanzu daga can a ke zuwa nan kasuwar Dawanau su kai can. Neja, Taraba, Jigawa, Katsina, Sikoto, Zamfara da Gombe duk a yanzu noma ya ja baya. Yawancin dalilan saboda tsoron ‘yan bindiga da kuma Boko Haram.

Kuma wani abu da na lura shi ne, waɗannan ƙungiyoyin na jinƙai na ƙasashen waje masu tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci, kashi 90 bisa 100 na kayan abincin duk a nan kasuwar Dawanau su ke sayen sa.

Kuma jami’an su duk sun zo nan sun tattauna da mu dangane da matsalar abinci, mun yi masu bayanai, kamar yadda na ke yi maka, don su san rahotannin da za su tattara domin a kauce wa matsalar.

Ita tsadar abinci fa ƙarancin sa ke haifar da ita. An kulle kan iyakokin ƙasa, alhalin wanda ake nomawa a cikin ƙasar bai wadata ba. Ka ga kuwa akwai matsala.

Ka ɗauki batun shinkafa. Da yawa waɗanda gwamnati ta ba ramce domin su yi masana’antu na cashe shinkafa, sun yi wasu harkokin da kuɗaɗen.

PTH: Ya za ka kwatanta yawan abincin da ake sauke lodin sa a kasuwar Dawanau a yanzu da kuma shekarun baya?

SANI ƘWA: Wannan kuma ai kowa ya san ya ragu sosai da sosai. Kira na kawai shi ne gwamanti ta riƙa sani waɗanda ta ke bai wa lamuni domin bunƙasa harkokin noma. Sannan kuma ina kira a bai wa masu sayar da kayan abinci jarin fita wurare masu nisa domin su sawo abinci daga wasu ƙasashe su kawo nan. Saboda a gaskiya lokacin korona ‘yan kasuwar Dawanau da dama sun cinye jarin su. Kuma gwamnati ba ta taɓa ba su wani tallafi ba.

Amma a yanzu mu na neman lamuni ta hannun Ofishin Ƙaramin Ministan Kasuwanci, Cinikayya da Zuba Jari. Muna fatan za mu samu.

Share.

game da Author