Tattalin arzikin Najeriya kan hanya ya ke tafiya ɗoɗar, ba tsallen-gada ya ke ba -Inji CBN

0

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya a kan hanya ya ke tafiya ɗoɗar, ba tsfiyar-kura ya ke yi ba.

Daraktan Sashen Tsare-tsaren Hada-hadar Kuɗaɗe na CBN, Hassan Mahmud ne ya bayyana haka.

Mahmud ya yi wannan bayani a Taron Tsakiyar Shekara na Nazarin Tattalin Arziki na shekarar 2021.

Ya ƙara da cewa duk da talalaɓiyar da ta fizgi tattalin arziki a cikin ƙasa da kuma na ƙasashen waje a faɗin duniya, har yanzu tattalin arzikin Najeriya na nan da tagomashin sa.

Taron wanda Cibiyar Nazarin Hada-hadar Kuɗaɗe (CIBN) ta shirya da haɗin-gwiwar Ofishin Ba. Adedipe Associates, an gudanar da shi ne a ranar Juma’a a Legas.

Ya ce da a ce an shawo matsalar faɗuwar ‘yan borin da naira ke yi da kuma matsalar tsaro, to tattalin arzikin Najeriya zai fara ganin canji da haɓɓaka sosai a ƙarshen 2021 da farkon 2022.

“Kuma idan hasashen da CBN ya yi kan ƙarfin tattalin arzikin cikin gida ya tafi a bisa saiti, kuma ba a samu dalilin da ya janyo aka sake ƙaƙaba dokar kullen korona ba, aka yi wa jama’a rigakafin korona, to ƙarfin tattalin arzikin cikin gida zai ƙaru da kusan kashi 3 bisa 100 nan da ƙarshen shekarar 2021.

“Kuma daga nan to za mu iya ganin malejin tsadar rayuwa ya sauka ƙasa sosai da kashi 13 bisa 100, maimakon ya riƙa hauhawa, kamar yadda NBS ta yi hasashe zai kasance a farkon 2022 ko tsakiyar 2022 ɗin.”

Daga nan Mahmud ya ce matsalar ƙarancin abinci ita ma za ta ragu idan aka daƙile matsalar tsaro.

Share.

game da Author