Mayaƙan ƙungiyar Taliban sun kwace babban birnin kasar Afghanistan, Kabul inda suka dunguma tare da shugabannin su zuwa fadar gwamnatin ƙasar.
Tun bayan janye sojojin ta da ƙasar Amurka ta yi daga ƙasar Afghanistan, mayakan Taliban suka fara yin nasara a yankunan kasar Afghanistan din.
Zuwa ranar Asabar sun kwace kusan duka jihohin kasar dake karkashin iko gwamnatin Asharf Ghani.
A ranar Lahadi kuwa ko da suka dira babban birnin kasar Kabul, salin alin suka ratsa ta cikin garin suka dunguma fadar gwamnatin ƙasar.
Hakan ya na nuna cewa ƙasar Afghanistan ta koma karkashin ikon kungiyar Taliban.
Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden ya sha alwashin cewa kasar ba za ta tura sojojinta kasar Afghanistan ba.
Taliban ta ce za ta kyale mata su rika aiki sannan kuma za su iya fita su kaɗai ba tare da rakiya ba.
Sannan kuma ta ce duk mai son ficewa daga ƙasar a barshi ta tafi kada a hana shi