Babban ma’aikacin jinya na asibitin kwakwalwa na gwamnatin tarayya dake Kware jihar Sokoto Umaru Jamo Julde ya yi karin haske game dalilan da ya sa matasa maza da mata ke ta’ammali da muggan kwayoyi sannan da barnar da yayi a yankin Arewacin kasar nan.
Julde ya ce babban matsalar dake saka matasa ta’ammali da muggan kwayoyi shine rashin kuzari ko ‘Anxiety’ da Turanci.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=2aHzK4ZuzCI&w=760&h=399]