Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya bayyana cewa matsalolin da Najeriya ke fuskanta ko kusa ba su kai tsamarin da har za a riƙa kwatanta ƙasar da halin da Afghanistan ke ciki yanzu ba.
Da ke ganawa da NAN bayan ya gana da wasu kafafen yaɗa labarai uku a Washington, babban birnin Amurka, Lai ya ce Najeriya ba ƙasa ce da ta durƙushe ba, ta na dai fuskantar matsaloli, kuma ana ta bakin ƙoƙarin daƙile su.
“Ƙasar da ta durƙushe ita ce wadda komai na ta ya tsaya cak ba ya aiki. Najeriya kuwa ko kusa ba haka take ba.” Inji Minista.
Ya je Amurka domin ganawa da manyan kafafen yaɗa labarai da nufin yi masu bayanan nasarorin da Najeriya ke samu a ƙoƙarin daƙile matsalolin tsaro.
Ya yi bayanin cewa ana samun nasarori sosai wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga.
“Idan aka dubi irin yadda ta kaya bayan Amurka ta shafe shekaru 20 a Afghanistan, ta kashe maƙudan kuɗaɗe da asarar dubban rayuka, amma Taliban sun sake ƙwace ƙasar.
A kan haka ne ya ce ya zama tilas a jinjina wa Shugaba Buhari wajen ƙoƙarin gwamnatin sa ta kakkaɓe ‘yan ta’adda, ba tare da ta gayyato wasu sojojin haya daga waje ba.”
Da ya koma kan batun fitar da Shugaba Buhari ke yi ganin likita a ƙasashen waje kuwa, Minista Lai ya ce, “fitar Buhari Ingila ganin likita ba alama ce ta durƙushewar kiwon lafiya a Najeriya ba.”
Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya kare dalili tare da bayar da hujjojin da su ka sa Shugaba Muhammadu Buhari ke fita Ingila ganin likita, duk kuwa da halin matsalar fannin kiwon lafiyar ƙasar nan ke fama da ita.
Lai ya yi wannan bayani a Washington, babban birnin Amurka, inda ya je domin ganawa da manyan kafafen yaɗa labarai.
Ministan ya je ne domin tallata masu ayyukan ci gaban da Gwamnatin Buhari ta samar a Najeriya.
Sannan kuma ya yi masu cikakken bayanin irin nasarorin da aka samu wajen ƙoƙarin daƙile ta’addanci, masu garkuwa da mutane da kuma mahara su kwasar dukiyoyin jama’a.
“Buhari na da ‘yancin ya fita neman magani ko ganin likita. Domin ba shi ne Shugaban Ƙasa na farko a Najeriya da ya riƙa fita waje ganin likita ba.
“Kuma Buhari ya na da likitan sa a waje, wanda ke duba shi, ya san ciwon sa, ya san maganin sa da kuma tsarin jiyyar sa. Saboda haka don me za a ce sai ya saki likitan sa na tsawon shekaru 30 ya kama sabo daban?
“Ko a matsayi na na Minista, idan a baya ina da likitan da ya san ciwo na kuma na fi yarda da shi, babu dalilin da zai sa a matsa min lamba sai na sake likita don na zama minista.”
A kan haka Lai ya ce ko ɗan wace ƙasa ce likitan da ya fi fahimtar ciwon mutum, to ya na da ‘yancin riƙe shi a matsayin likitan sa.
Sannan kuma ya nuna cewa fitar da Buhari ke yi ba hujja ce da wasu ke cewa harkar kiwon lafiya a Najeriya ta durƙushe ba.
Cikin gidajen jaridun da Lai ya gana da su, har da BBC Radio da Talbijin, Bloomberg da kuma Politico.
Sannan kuma ya gana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, a ofishin sa da ke Washington.
[11:15, 8/19/2021] Ashafa Daughter Numbers: SAD! Tun jiya Oti ta yi min reply cewa kuɗi fa ba zai samu ba. Kawai na nema a wani wuri!
Discussion about this post