SUNAYE: Ɗalibai da malaman Kwalejin Bakura da mahara suka sace

0

Rajistaran Kwalejin Koyon Aikin Noma Aliyu Bakura ya fidda sunaye ɗaliban da mahara suka sace, da malaman da maharan suka tafi da su.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ƴan bindiga suka sace ɗaliban Kwalejin Bakura da wasu daga cikin malaman kwalejin a cikin makon jiya.

Rajistaran kwalejin Aliyu Bakura ya bayyana cewa maharan sun sace ɗalibai 15 da wani malami da matar sa.

” Ƴan bindigan sun shigo makarantan ɗauke manyan makamai. Sun kashe jami’an tsaro hudu har da ƴan sanda.

Har yanzu akwai ɗalibai da dama dake tsare hannun ƴan bindiga ba a sako su ba.

Ga sunayen

Isma’il Lawali, Salim Salisu, Kabiru Lawali, Yasir Lawali, Awaisu Jabir, Aminu Umar, Abba Aliyu, Aminu Adamu, Usman Umar da Umar Haruna.

Sauran sun haɗa da Usama Lukman, Abdurahman Lukman, Junaidu Yunusa, Abdullahi Bala da Jamilu Kwatarkwashi.

Sannan kuma malaman da aka tafi da sun haɗa Mustapha Abdullahi Mafara, Nusaiba Gambo, Hannatu Gambo and Hibbatu Gambo.

Maharan sun kashe Sani Mohammed Mafara, Lawali Sani Jatau da Sufeton ƴan sanda, wanda dukkan su masu tsaren ƙofar shiga makarantar ne.

Share.

game da Author