SUN YI AMAI SUN LASHE: Gwamnati Kaduna ta ce babu komawa makarantu duk da karyata labaran da aka ce ta faɗi haka a baya

0

A cikin wata sanarwa wanda gwamnatin Kaduna ta fidda ranar Juma’a, ta yi kira ga mutanen Kaduna su ci gaba da hakuri da maganar komawar yayan su makarantu domin ci gaba da karatu, domin sai fa lokacin da gwamnati ta gamsu an samu saukin matsalara tsaro a jihar.

Kwamishinan Tsaro da na Ilimi, Samuel Aruwan da Muhammed Shehu sun bayyana cewa har yanzu jami’an tsaron a jihar ba su gama tsatssefe dazukan jihar domin fidda yan bindiga ba tukunna saboda haka a ci gaba da zama a gida tukunna.

Idan ba a manta ba jaridun Najeriya sun ruwaito a makon jiya cewa gwamnatin jihar ta dage komawa makarantun jihar sai Illa-Ma-Sha’Allah, amma kouma daga baya ta karyata sanarwar cewa ita ba ta fidda irin wannan sanarwa ba, kuma tana nan a kan bakan ta na na cewa za a dawo makarantu ranar 9 ga Agusta.

Sanarwar ranar Juma’a ta ce ba za a bude makarantun jihar ba sai jami’an tsaro sun ba gwamnati shawarar a bude makarantun sannan zata sanar da ranakun da za a bude su.

Ba makarantun jihar ba kawai, hatta wasu wurare da ake manyan ayyuka wanda kuma akwai matsalar tsaro a wuraren, duk za a dakatar da ayyukan sai an samu natsuwa da tabbacin tsaro a wuraren sannan za a ci gaba da ayyuka.

A karshe Kwamishina Aruwan ya yaba wa dakarun tsaro dake aiki tukuru a jihar.

Share.

game da Author