Sojojin Nijar na batakashi da ƴan bindiga a Jibia, Jihar Katsina

0

Sojojin Kasar Nijar sun biyo wasu gungun ƴan bindiga har cikin dazukan da ke kewaye da garin jibia, jihar Katsina domin gwabzawa da su ranar Talata.

Mustapha Aliyu dake wakiltar karamar hukumar Jibia a majalisar dokokin jihar ya bayyana wa wakilin mu cewa ƴan bindigan sun sace sanun wasu makiyaya a kauyen ƙasar Nijar, daganan sai sojojin ƙasar suka dira musu har cikin yankin jibia inda aka yi ta kwabzawa a tsakanin su.

Ƴan bindigan sun sace shanun wasu mutanen kasar Nijar, suka shigo da su Najeriya. Hakan yasa sojojin Nijar suka biyo su har Najeriya domin kwato sahnun.

Bayan rauni da kashe soja ɗaya da maharan suka yi, dakarun Nijar sun koma sun sake shiri suka dawo cikin dajin da motocin sojoji akalla 17.

Mazauna sun ce sun rika jin luguden wuta da ƙugin albarusai ada bama-bamai wanda sojojin Nijar ɗin suka antaya wa waɗannan ƴan bindiga babu ƙaƙƙautawa.

Share.

game da Author