Shugaban majalisar Kaduna, Honarabul Yusuf Zailani tare da daruruwan ƴan uwa da makusanta sun halarci sallar jana’izar marigayiya Hajiya Maimunatu a Zaria.
Marigayiya Maimunatu kakace ga Kakakin majalisar Kaduna, Yusuf Zailani. Ita ce ta haifi mahaifin kakakin majalisar jihar Kaduna, Ibrahim Zailani, wanda ɗan uwa ne ga tsohon babban maishari’a na jihar Kaduna, Tanimu Zailani da tsohon babban sakataren a ma’aikatar Harkokin Ƙananan hukumomin jihar Kaduna, Mahmud Zailani.
Ta rasu tana da shekaru 105.
Sarkin Zazzau, maimartaba Ahmed Bamalli ya harci jana’zar.