Sarkin Argungu a Jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Mera zai naɗa Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi.
Bikin naɗin sarautar wanda za a yi a ranar 25 Ga Satumba, ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Kamfanin Dillancin Labarai ya buga bisa sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Ƙasa (NIHOTOUR), Ahmed Sule.
Tun a ranar 7 Ga Maris Sarkin Argungu ya sanar da bai wa Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi, amma ba a bayyana ranar da za a yi bikin naɗin ba, sai yanzu.
Sarki Mera ya sanar da sarautar kan Minista Lai Mohammed a Abuja cikin 2020, yayin da ya gabatar da tsarin shirin Bikin Kamun Kifi na Argungu, wanda aka gudanar a ranakun 11 zuwa 14 Ga Maris, 2020.
Sanarwar ta ce a yanzu shirye-shirye sun yi nisa matuƙa domin ganin bikin naɗin ya yi armashi.
Sarkin ya ce an yanke shawarar naɗa Minista Lai sarautar Kakakin Kebbi, bayan Majalisar Masarautar ta zauna ta yanke hukuncin amincewa, bisa irin ƙoƙari da himmar Minista wajen yayatawa da isar da kyawawan al’adun Najeriya a cikin duniya.
“Hakan kuwa ya haifar da samar da ayyukan yi, kuɗaɗen shiga da wayar da kan jama’a musamman matasa game da muhimmancin bukukuwan al’adu da kayan amfanin gargajiya.
“Sannan kuma Masarautar Argungu ta lura da irin ayyukan ɓunƙasa ƙasa tare da ayyuka tuƙuru da ministan ya ke gudanarwa da aiwatarwa a ofishin sa na minista.
Sanarwar ta ce naɗin da za a yi wa Lai a ranar 25 Ga Satumba, za ta zama ɗaya daga cikin shagulgulan da za a yi a wurin Taron Tunawa da Ranar Yawon Shaƙatawa ta Duniya, wadda ta zo daidai da ranar 27 Ga Satumba, da za a yi Jihar Kebbi.