Sama da mutum 112 Ƴan bindiga suka kashe a Kaduna da Filato cikin kwanaki 30

0

Gwamnatin Najeriya ta nuna gazawarta wajen daƙile hare-haren ƴan bindiga da kisan da suke yi babu ƙaƙƙautawa musamman akan manoma da makiyaya a wasu daga cikin yankunan jihar Kaduna a Filato.

Kungiyar Amnesty International ce ta wallafa rahoto akan abubuwan da suka auku a waɗannan jihohi biyu cikin kwanaki 30 da suka wuce.

Akalla mutum 112 aka kashe sannan aka yi garkuwa da mutum sama da 160, baya ga dubban mutane da suka rasa matsuguni a sanadiyyar hare-haren ƴan bindiga daga tsakanin farkon watan Yuli zuwa farkon Agusta.

” Abin da muka gano sun haɗa da ramuwar gayya ne ya yi tsanani a tsakanin mazauna wuraren da hare-haren ya ki ci yaki cinyewa. Ba a ɗauki wasu kwararan matakai don ganin an kawo ƙarshen waɗannan kashe-kashe da rashin zaman lafiya da ake fama da shi a musamman waɗannan jihohi biyu.” In ji Osai Ojigho, Darektan Kungiyar.

Binciken Amnesty ya nuna cewa akalla mutum 78 ne aka kashe sannan aka yi garkuwa da mutane 160 tsakanin 3 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta a jihar Kaduna, harda ɗalibai 121 ƴan makarantan Bethel da aka sace.

A jihar Filato kuwa, mutum 34 ne aka kashe da suka haɗa da wasu makiyaya 7 da aka bi su har gidajen su aka kashe ranar 1 ga watan Yuli. Sannan kuma aka bi wasu makiyaya biyu har kauyen su suma aka yi musu dukan tsiya.

Bayan haka sai kuma waɗanda aka kashe wa ƴan uwa suka afka wa wasu ƙauyuka domin daukar fansar kisar ƴan uwan su da aka kashe. A wannan hari an kashe mutum 17, sannan daruruwan mutane sun rasa matsugunin su.

A karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen samar da tsaro ga mutanen kasar nan. Sakaci da rashin maida hankali da gwamnati ba ta yi ba yasa ake samun yawaitar hare-hare da daukar fansa.

Share.

game da Author