A wata sanarwa wanda Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fidda ranar Litini, ta kunshi bayanai da sunayen wasu mutane 15 da jami’an tsaro da ke aiki a jihar suka ceto daga hannun ƴan bindiga a karamar hukumar Jema’a.
Aruwan ya ce jami’an tsaro sun ceto wasu matafiya da ƴan bindiga suka sace amma kuma kafin su nausa da su maboyar su jami’an tsaro sun dira, sun ceto matafiyan.
An bada sunayen waɗanda aka sace kamar haka:
– Maisaje Pam
– Samuel Peter
– Ziyau Abdul
– Henry Dabo
– Abduljabar Auwal
– Muhammad Ali
– Dama Dabo
– Ramatu Aminu
– Muhammad Sani
– Abdullahi Muhammad
– Bashar Garba
– Abubakar Musa
– Saad Yakubu
– Maryam Ibrahim
– Lami Bitrus
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA, ta buga labarin harin da ɗaukar fansa da wasu mazauna kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf su kayi a Kaduna.
Wannan hari ya yi sanadiyyar rayukan mutane sama da 15.