RIKICIN YARABAWA DA HAUSAWA A OGUN: Yadda rayukan mutum bakwai suka salwanta, aka ƙone tirelolin Dangote 11

0

Aƙalla an ƙone manyan motocin ɗaukar kaya na Dangote Cement 11, a ranar Talata, yayin da hasalallun matasan Yarabawa su ka banka masu wuta.

An ƙone motocin ne yayin da su ke ajiye a ƙofar shiga Masana’antar Dangote Cement, a garin Ibese, Ƙaramar Hukumar Yewa ta Arewa, Jihar Ogun.

Rikicin ya samo asali ne daga tankiya tsakanin ‘yan acaɓa, waɗanda akasarin su Hausawa ne ‘yan Arewa, da kuma jami’an karɓar kuɗaɗen harajin ta hanyar sayar da tikiti ga ‘yan acaɓa.

Rigima ta fara kaurewa yayin da aka ƙara kuɗin tikiti daga naira 600 zuwa naira 800.

Waɗanda faɗan ya yi muni a gaban su, sun tabbatar da cewa rikicin ya rikiɗe zuwa tantagaryar rikicin ƙabilanci tsakanin Yarabawa da Hausawa, a daidai kusa da masana’antar siminti ta Dangote Cement da ke Ibesi.

Ganau ya tabbatar da cewa zuwa ranar Talata dai an tabbatar da kisan mutum bakwai.

Lokacin da wakilin PREMIUM TIMES ya je wurin da aka yi rikicin a ranar Laraba, ya ga ƙonannun motocin Dangote Cement guda bakwai a ƙone ƙurmus.

Wani mazaunin wurin mai suna Hamzat Ibrahim, ya shaida masa cewa an fara rikicin tun a ranar Litinin a kan farashin sayar da tikitin karɓar haraji a hannun ‘yan acaɓa masu haya da babura.

‘Hausawa sun doki mai sayar da tikiti. Su kuma matasan yankin su ka riƙa ƙone kayayyakin Hausawa, har su ka kai ga ƙone motocin Dangote.

Ɗan Majalisar Jihar Ogun mai wakiltar Yewa ta Arewa 1, ya ce laifin gwamnati ne da kuma laifin kamfanin Dangote.

“Ta yaya za a ce kamfanin Ɗangote ba shi da garejin da za a riƙa ajiye motocin sa. Da su na can a ƙeɓance da ba a je an yi masu ta’adi ba. Saboda haka ya kamata Gwamna da Dangote su zauna su samar da wurin ajiye motocin kamfanin sa da gaggawa.”

Daga nan sai ya yi kira da a ƙirƙiro sarautar gargajiya a garin, ta yadda shugabanni gargajiya su riƙa sasanta ƙananan matsalolin cikin jama’a, kafin a yi sakacin da zai kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Kakakin ‘Yan Sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar wa wakilin mu faruwar lamarin, amma bai bayyana adadin yawan mutanen da su ka rasa rayukan su ba.

Share.

game da Author