RIKICIN JAM’IYYA: Gwamnonin PDP sun ƙaryata zargin sun nemi Uche Secondus ya sauka daga shugabancin jam’iyya

0

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun ƙaryata zargin da aka yi masu cewa sun nemi Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Uche Secondus ya sauka daga shugabancin jam’iyya.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Cyril Maduabum ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, ya ce gwamnonin PDP ba su nemi Secondus ya sauka ba, amma dai sun nuna goyon baya ne ga Mataimakin sa na Shiyyar Kudu, Yemi Akinwonmi, wanda shi Secondus ya damƙa wa ragamar riƙo, bayan da Babbar Kotun Fatakwal ta dakatar da shi.

An dai zargin gwamnonin da umartar Secondus ya sauka, duk kuwa da maida shi kan kujerar sa da Babbar Kotun Birnin Kebbi ta yi.

Premium Times ta buga yadda Kotun Birnin Kebbi ta maida Secondus kan kujera, bayan dakatarwar da Kotun Fatakwal ta yi masa

Babbar Kotun Birnin Kebbi ta maida Shi Jam’iyyar PDP, Uche Secondus a kan kujerar sa a ranar Alhamis.

Kotun ta maida shi ne kwanaki uku bayan Babbar Kotun Fatakwal a Jihar Ribas ta dakatar da shi, a wata ƙara da aka maka shi a ranar Litinin.

Wasu mutane biyu mambobin jam’iyyar PDP uku da su ka haɗa da Yahaya Usman, Abubakar Muhammad da kuma Bashar Suleman ne su ka shigar da ƙarar a Babban Kotun Kebbi, a ranar 25 Ga Agusta, 2021, su ka nemi a soke dakatarwar da Babbar Kotun Fatakwal ta yi wa Secondus.

Lauyan mutanen uku mai suna Ibrahim Jibril, ya riƙa kotun ta dubi ƙarar da su ka shigar, a maida Uche Secondus kan shugabancin PDP.

Mai Shari’a Nusirat Umar ta amince kuma ta maida shi, bisa hujjoji da dalilan da ta bayar. Ta ce ya ci gaba da kasancewa kan muƙamin sa har sai hukuncin da kotu ta zartas kan sa tukunna.

Wasu Gwamnonin PDP ne da mambobin jam’iyyar su ka kitsa tuggun cire shi, bisa zargin shugabancin sa ya kawo rigima a cikin jam’iyya, har wasu gwamnoni, sanatoci da manyan ‘yan jam’iyya na komawa jam’iyyar APC.

Hukuncin da Kotun Kebbi ta yanke na kuma nuna cewa Sanata Nazifi Suleiman da ya kira kan sa shugaban riƙo, shi ma an haramta shugabancin sa na riƙo kenan.

Share.

game da Author