Rashin So tsakanin wasu ma’aurata a Kaduna ya sa sun garzaya kotu ta raba su

0

Kotun Majistare da ke Maganin Garin dake jihar Kaduna ta raba auren Bilkisu Bawale da mijinta Bello Musa saboda rashin son juna da ba su yi kmuma.

Alkalin kotun Nuhu Falalu ya yanke hukuncin cewa Bilkisu za ta maida wa Musa kudin sadakinta naira 20,000.

Lauyan dake kare Bilkisu M.B. Alhassan ya ce Bilkisu tana nemi kotu ta raba auren ta da Musa saboda bata kaunar sa kuma.

“Musa bai yi mun laifin komai ba kuma yana biya min duk hakkunan aure da suka rataya a kan sa a matsayinsa na miji na amma kuma a gaskiya son sa ya fice min a zuciya kwata-kwata, bana son sa.

“A dalilin haka ya sa nake so a raba auren mu saboda kada in fada cikin wani mummunar hali, mula’iku su rika tsine min.

Lauyan dake kare Musa Usman Nda-Liman ya ce sun amince kotu ta raba auren.

Share.

game da Author