Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya wani bashin da aka yi iƙirarin ana bin jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774.
Adadin bashin ya kai dala miliyan 418, kwatankwacin naira biliyan 159 da ya amince a biya wasu mutum shida, duk kuwa da cewa Gwamnonin Najeriya sun daɗe su na nuna wa Buhari cewa babu tabbaci ko wata ƙwaƙƙwarar shaida ko hujjar an yi ayyukan a jihohi har na waɗannan adadin maƙudan kuɗaɗe.
A ranar Talata PREMIUM TIMES ta ci karo da wani umarni da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta bai wa Ofishin Kula da Basussuka (DMO), cewa ya fara bayar da takardar alƙawarin biyan kuɗaɗe ga waɗanda su ka yi iƙirarin cewa su na bin jihohin da ƙananan hukumomi waɗannan kuɗaɗen.
Hakan dai ya na nufin Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba amincewa a biya bashin kenan.
Wannan mataki da Buhari ya ɗauka ya saɓa da shawarar da Gwamnonin Najeriya su ka sha bayarwa cewa a fara gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike a ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan, domin a tabbatar da sahihancin ayyukan da masu iƙirarin bin bashin su ka ce sun yi, amma ba a biya su ba.
Sai dai kuma duk da wannan damuwa da gwamnonin su ka nuna, Buhari ya amince a biya kuɗaɗen tare da yin fatali da shawarar ta su.
Za a biya su kuɗaɗen a tsawon shekaru 10, wato daga nan zuwa 2031. Za a riƙa cira daga cikin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa Jihohi da Ƙananan Hukumomi duk bayan wata ɗaya.
Wasiƙar umarnin da aka ba Ofishin DMO dai an rubuta ta ne a ranar 12 Ga Agusta, 2021. Dama kuma tun a ranar 11 Ga Janairu Buhari ya amince a fara biyan kuɗaɗen, amma wata tankiya da gwamnoni ta sa ya dakatar.
Waɗanda za a biya kuɗaɗen dai su shida sun haɗa da tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ned Nwoko, wanda ya ke kafa hujja da umarnin biyan wanda Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/148/2017.
Nwodo na neman a biya shi dala miliyan 142,028,941.
Sai kuma wasu mutum uku da ke neman a biya su dala miliyan 143,463,577.76 a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/CV/2129/2014.
Su ukun sun haɗa da Riok Nigeria Ltd, Orji Nwafor Orizu da wani mai suna Olaitan Bello.
Wanda ya fi saura kason kuɗaɗe a cikin su shi ne Iseghoghi Edwards, mai dala miliyan 159. A bisa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta zartas mai lamba FCT/CV/1545/2015.
Akwai kuma kamfanin wani mai suna George Uboh, wanda zai karɓi dala miliyan 47,831,920.
Salsalar Zargin Gidogar Da Gwamnonin Najeriya Su Ka Ce An Tafka A Batun Biyan Bashin:
Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda Minista Malami ya ƙi jin gargaɗin zargin harƙalla, ya riƙa ƙoƙarin a biya bashin naira biliyan 159.
An shafe shekaru ba ɗaya ba, ba biyu ba, Ministan Shari’a Abubakar Malami na bijire wa gargaɗin da ake yi masa cewa wasu kuɗaɗe da ya ke ta ƙoƙarin ganin an biya daga cikin kason kuɗaɗen Jihohi da Ƙananan Muhumomi har dala milyan 418 (naira biliyan 159), akwai gidoga a cikin lamarin.
Kuɗaɗen dai an ce wai bashi ne wasu ‘yan kwangila da jami’an tuntuɓa ke bin jihohi da ƙananan hukumomi.
Amma duk da gargaɗin da aka rika yi wa Malami, ciki kuwa har da rahoton da EFCC ta damƙa masa, wanda ta nuna cewa bashin haramtacce ne, ba gaskiya ba ne, shi kuma Minista Malami ya rufe ido sai matsa lamba ya ke yi domin ganin an biya waɗanda aka ce wai su na bin bashin, ta hanyar riƙa cirar kudade ana biyan bashin daga kuɗaɗen da Gwmnatin Tarayya ke bai wa Johohi da Ƙananan Hukumomi a duk ƙarshen wata.
Wannan jarida ta mallaki kwafe-kwafe na takardun da su ka riƙa karakaina da ke nuna yadda Malami ya rufe ido ya ke ta sharce gumin ganin lallai a biya kuɗaɗen, duk kuwa da cewa hatta Ƙungiyar Gwamnoni ta Najeriya, NGF ta bayyana masa cewa binciken ƙwaƙwaf ne kadai zai iya tabbatar da sahihancin bashin ko bogi da gidoganci ne kawai.
‘Yan Ƙaƙuduba Uku:
Sauran mutane biyun da su ka haɗa kai da Minista Malami domin ganin an biya kuɗaɗen ido-rufe, sun haɗa da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da kuma Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed.
Gungun Wasu ’Yan Gidoga:
Wato akwai wasu ’yan dillancin gidoga da ke iƙirarin su ne wakilan masu bin bashin, waɗanda wakilan mu su ka ji cewa sun yi ƙoƙarin su bai wa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi toshiyar bakin dala milyan 40, domin ya haƙura, ya daina tirjiya, ya amince a biya bashin kawai.
Amma Gwamna Fayemi dtin na Jihar Ekiti bai amince ba, ya ƙi karɓar tayin da su ka yi masa, inda ya tsaya kai da fata cewa lallai sai dai a yi ƙwaƙƙwaran binciken ƙwaƙwaf domin a gano gaskyar lamarin.
Sai dai kuma bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa wannan ƙaƙudubar, an riƙa ɗaukar nauyin buga wasu bayanan ɓata suna ga Gwamna Fayemi a cikin kafafen yaɗa labarai.
Cewa aka riƙa yi wai Fayemi an ƙi amincewa da roƙon da ya yi na a datse kashi 10 cikin 100 na bashin.
Salsalar Wannan Hukuncin Biyan Bashi:
Batun wannan bashi da ake tankiya da tababar sa, ya samo asali ne daga wani hukuncin da kotu ta yanke cewa wasu ’yan kwangila da jami’an tuntuɓa na bin jihohi da ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan basussuka.
Wasu ’yan gidoga su ka yi iƙirarin cewa su jami’an tuntuɓa ne su ka ce sun taimaka wa ƙananan hukumoni da jihohi domin su karɓo kuɗaɗen su da aka cira fiye da kima tsakanin 1995 da 2002 domin biyan bashin Paris Club.
Wasu ‘yan kwangila kuma daga cikin su wai sun yi wa ƙananan hukumomi 774 ayyuka bashi, saboda zaman jiran tsammanin za a biya kuɗaɗen Paris Club a biya su daga ciki.
A baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Najeriya, ALGON ya nuna goyon bayan a biya kuɗaɗen.
Buhari Ya Sani Ya Yi Shiru:
PREMMIUM TIMES ta buga labari a cikin Janairu, yadda Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara tare da sanar da shi cewa cewa kada ya bari a biya kuɗaɗen, domin babu wata ƙwaƙƙwarar hujjar an yi ayyukan bashin.
Sai dai kuma duk da wannan gargaɗin Buhari bai taka wa su Malami burki ba
Sai ma da ta kai ga Malami ya samu saƙonnin gargaɗi daga wurare uku, ciki har da EFCC su na shaida masa cewa kada ya shiga gaba a biya bashin, domin akwai gidoga a cikin lamarin.
Cikin waɗanda su ka gargaɗi Minista Malami har da Shugaban ALGON na baya-baya, wanda shi ma ya nuna cewa kamfanonin tuntubar masu cewa su ne dillalan waɗanda ke bi bashi, ba su san da zaman su ba.
Yayin da su Malami su ka matsa lamba har Buhari ya sa hannu kan cakin kuɗin alƙawarin biya (promisory note), a ranar 4 Ga Disamba, 2020, su ma Gwamnomin daga baya cikin Janairu sun samo wani sabon umarni daga Buhari cewa kada a biya kuɗaɗen, har sai an yi ƙwaƙƙwaran bincike. Amma yanzu kuma Buhari ya amince a biya kuɗaɗen, ba tare da ya koma ta kan shawarar da Gwamnonin Najeriya su ka ba shi ba.
Ƙaryar Kwaram-kwaram Ta Ƙare:
Yanzu dai duk wani ƙoƙari da Gwamnonin Najeriya da Shugabannin ALGON 774 na Ƙananan Hukumomin Kasar nan kakaf su ka yi don kada a biya kuɗaɗen, ya tashi a iska, domin alƙalami ya bushe, tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya kuɗaɗen.
Discussion about this post