Kwamishin Ysaro da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samu rahoto daga jami’an tsaro da ke aiki a jihar cewa kungiyar ƴan bindiga biyu sun kicime da faɗa bayan sun samu rashin jituwa wajen rabon kuɗi.
Aruwan ya ce wani gogarman ƴan bindiga mai suna Godon Mota ya shiga ƙauyen Garke dake ƙaramar hukumar Giwa, sai dai kuma shigar sa ke da wuya sai ya ci karo da wasu gungun ƴan bindigan da suka rukume a tsakanin su.
A wannan rikici sai da suka kashe mutum tara a tsakanin su.
Majiya ta shaida cewa, Godon Mota da dakarun sa sun dira garin Garke ne a dalilin saɓani da ya shiga tsakani wajen rabon kuɗaden fansar mutanen da aka sace tsakanin kungiyoyin biyu.
Aruwan ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike akai bayan tabbatar da aukuwar abinda ya kawo rashin jituwa tsakanin maharan da kuma yawan waɗanda suka mutu.