Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ƙaryata rahotannin da su ka nuna cewa jami’an EFCC sun kama shi a ranar Asabar.
Saraki ya je tabbas ya je ofishin EFCC, amma shi ya kai kan sa, ba a kama shi ba, kuma bai kwana a ofishin su ba.
Yayin da Saraki ya ke bayani ta bakin kakakin yaɗa labarai na Saraki, wato Yusuf Olaniyonu ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar.
“Saraki ya ziyarci Hedikwatar EFCC don raɗin kan sa. Ba kama shi aka yi ba, ba tasa ƙeyar sa aka yi ba, kuma bai kwana can a tsare ba. A gidan sa ya kwana.” Inji Kakakin sa.
Saraki dai ya shafe sa’o’i masu yawa ana yi masa tambayoyi a ranar Asabar a hedikwatar EFCC da ke kusa da hedikwatar Jami’ar NOUN, a Abuja.
An yi ta antaya masa ruwan tambayoyi ne dangane da zargin haɗa baki da wasu kamfanoni na bige da nufin karkatar da kuɗaɗe.
Majiyar da ke da masaniyar zuwan Saraki ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Saraki tabbas ya sha tambayoyi dangane da zarge-zargen da aka yi masa.
Daga baya EFCC ta fitar da sanarwa cewa ta gayyaci Saraki domin ya amsa wasu tambayoyi kan zargin rashawa da karkatar da kuɗaɗe.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Saraki, Yusuf Olaniyonu ya ce Saraki bai kwana a hannun EFCC ba, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai su ka tsegunta. Ya ce kuma dama shi ya kai kan sa, ba ƙeyar sa aka tasa ba.
“Idan ba a manta ba, ai Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin a daina take ‘yancin Saraki, tun a lokacin tsohon shugaban EFCC, har sai an kammala jin ta bakin kotun tukunna.
“To a zaman da aka yi na ranar 14 Ga Yuli, hukumar ta ce hukuncin da kotun ta yanke ya na kawo mata tsaiko ga aikin ta.
“Kan haka ne ya je ofishin ya nuna masu duk lokacin da su ke buƙatar sa, zai iya zuwa domin ya warware masu zare da abawa dangane da binciken da su ke yi a kan sa.” Inji Olaniyonu.
Discussion about this post