Babban Akawun Najeriya ya ce Adolphus Aghughu ya bayyana cewa babu wasu kuɗaɗe da su ɓace daga Asusun Gwamnantin Tarayya har naira tiriliyan 4.9 ko makamancin haka.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Ofishin Babban Akawun Tarayya, Eme Oqua ya fitar kuma ya sa wa hannu a ranar Alhamis, ya bayyana cewa kuɗin ba su ɓata ba, lissafi ne dai bai haɗu cif-cif ba lokacin da wasu bayanai su ka fita.
Ya maida wannan raddi ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa naira tiriliyan 4.9 sun tashi daga Asusun Gwamnantin Tarayya, sun lula sararin samaniya, har sun shige duniyar bil Adama.
Batun ya taso bayan Babban Akawun Tarayya Aghughu ya bayyana gaban Kwamitin Kuɗaɗe a Majalisar Tarayya, inda ya yi bayanin yadda aka samu tsaikon Bayanan Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya na 2019.
A kan haka ne sai sanarwar ta nanata cewa “Babban Akawun Tarayya bai ce kuɗaɗe sun salwanta ba, amma bayanan da ya yi na nufin ta yiwu wasu ‘yan kura-kurai ko rashin haɗa adadin ƙididdiga aka samu, ta yadda alƙaluman ba su kammala ba a lokacin bincike. Amma kuɗi ba su ɓace ba.”
“Saboda haka a yi kula cewa Bayanan Ƙididdigar Kuɗaɗe na 31 Ga Disamba, 2019 na nan cif-cif.” Inji sanarwar.
Hakan dai ya faru ne daidai lokacin da Majalisar Tarayya ta nuna damuwar ganin yadda Gwamnatin Tarayya za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.62, alhali kuma wasu hukumomin gwamnati ba su shigar da kuɗaɗen shigar su a cikin aljihun Gwamnatin Tarayya.
Discussion about this post