Na yi wa matsalar tsaro tofin ƙulumboto da tsatsube-tsatsuben samun zaman lafiya a kasar nan – Basarake

0

Yayin da jami’an tsaro na ɓangarori daban-daban ke fama da ƙalubalen matsalar tsaro tsawon shekaru 12, shi kuma Basarake Ganiyu Latonu da ke Masarautar Ife, ya yi iƙirarin cewa ya yi wa matsalar tofin ƙulumboto da tsatsube-tsatsuben samun zaman lafiya a ƙasar nan baki ɗaya.

Ganiyu wanda ke riƙe da sarautar Ogegbo na Ibonwon da Jihar Lagos, ya yi wannan bugun ƙirjin ne a lokacin da wasu manyan ɗaliban Jam’iar Ibadan su ka kai masa ziyarar neman tubarraki, a Eredo, yankin Epe da ke Jihar Legas.

“Na yi amfani da harshe na, ya yi addu’a da ƙulumboto domin a samu zaman lafiya a masarauta ta da ƙasar nan baki ɗaya.

“Na yi tawassuli da Oduduwa tare da neman tubarrakin sa wurin Ubangiji ya kara wanzar da zaman lafiya a ƙasar nan da masarauta ta.”

Basaraken ya roƙi ubangiji ya ci gaba da shiryarwa da kuma kare shugabannin mu.

Ya ce matsalar tsaron ƙasar nan da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ba, an kusa kawo ƙarshen ta idan aka yi amanna da irin ƙarfin ƙulumboto da surkullen addu’o’in da ya yi wa ƙasar nan.

Sarkin wanda makon jiya ne ya gaji gadon sarautar daga mahaifin sa, ya roƙi Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ƙara masa daraja, zuwa Basarake mai daraja ta ɗaya.

Share.

game da Author