Mutum 93 Korona ta yi ajalin su ranar Lahadi a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 93 da suka rasu a dalilin kamuwa da cutar Korona ranar Lahadi a Najeriya.

Idan ba a manta ba a ranar Asabar hukumar ta fidda alkalumar mutum 54 da suka rasu a dalilin korona a kasar nan.

Yaduwar cutar

Legas – 72,445, Abuja-20,534, Rivers-10,169, Kaduna-9,225, Filato-9,179, Oyo-8,082, Edo-5,341, Ogun-5,341, Kano-4,044, Akwa-ibom-3,984, Ondo-3,968, Kwara-3,556, Delta-2,914, Osun-2,691, Enugu-2,556, Nasarawa-2,414, Gombe-2,239, Katsina-2,164, Ebonyi-2,048, Anambra-2,046, Abia-1,794, Imo-1,710, Bauchi-1,553, Ekiti-1,447, Benue-1,413, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,062, Bayelsa-1,029, Niger-966, Sokoto-796, Jigawa-562, Yobe-501, Cross-Rivers-475, Kebbi-458, Zamfara-251, da Kogi-5.

Allurar rigakafi

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta bude wuraren guda 88 domin yi wa mutane allurar rigakafi da ruwan maganin AstraZeneca a jihar.

Shugaban fannin kula da kiwon lafiyar mutane na ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Tunbosun Ogunbanwo ya ce gwamnati ta yi haka ne domin wadanda suka yi allurar rigakafin da ruwan maganin AstraZeneca a zangon farko su samu yin allurar zango na biyu.

Ogunbanwo ya ce za a fara yi wa mutane allurar rigakafin daga ranar 30 ga Agusta zuwa 24 ga Satumba.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya hana Musulmai da Kiristoci shiga masallatai da coci-coci ba tare da katin shaidar an yi wa mutum rigakafin korona ba.

Wannan doka ta shafi shiga bankuna da sauran wuraren da dandazon jama’a ke taruwa.

Obaseki ya yi wannan bayani a Benin, babban birnin jihar, a lokacin da ya ke ƙaddamar da fara yin allurar korona kashi na 2 a jihar.

Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum miliyan 3,966,005 allurar rigakafin korona inda daga ciki mutum sama da miliyan biyu sun yi rigakafin zango na biyu.

Share.

game da Author