Alkaluman yaduwar cutar korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa mutum 189,661 sun kamu da cutar a kasar nan.
Adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya karu bayan an samu karin mutum 753 da suka kamu da cutar a Najeriya ranar Alhamis.
A wannan rana kuma an samu karin mutum 5 da cutar ta yi ajalin su a kasar nan inda hakan ya kawo jimlar yawan mutane da cutar ya kashe zuwa 2,200.
Zuwa yanzu mutum 166,560 sun warke sannan mutum 12,000 na dauke da cutar a yanzu haka.
Bayan haka mutum 364 sun kamu a jihar Legas, Akwa Ibom-141, Oyo-74, Rivers-46, Abia-38, Ogun-24, Kwara-20, Abuja-12, Ekiti-10, Delta-9, Edo-6, Filato-5, Imo-3 da Bayelsa-1.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin korona na Moderna guda 177,600 a tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Kwalaben maganin rigakafi 177,600 da Najeriya ta karba na daga cikin kwalabe miliyan 29.8 da ya kamata za a kawo.
Gwamnati ta ce za ta fara yi wa mutane allurar rigakafi zango na biyu ranar Litini.
Zuwa yanzu mutum sama da miliyan uku ne suka bada kansu domin yin allurar rigakafin korona a kasar nan.