Mutum ɗaya daga cikin mutane 6 a Kano na ta’ammali da ko Tramol, Kodin ko murza ganyen Wiwi – Buba Marwa

0

Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa ya bayyana cewa akwai mutum akalla miliyan biyu dake ta’ammali da muggan kwayoyi a jihar Kano.

Buba Marwa ya furta wannan kalamai a lokacin da ya ke jawabi a fadar gwqmnatin Kano da ya kai wa gwamnan jihar Abdullahi Ganduje Ziyara.

“A Jihar Kano adadin yawan mutanen dake ta’ammali da muggan kwayoyi sun kai akalla mutum miliyan 2 wanda kashi 16 kenan cikin 100.

“Hakan na nuna cewa cikin mutane shida mutum daya na ta’ammali da kwaya ko wani nauin abu dake sanya maye. Sannan kuma matasa ƴan shekara 15 ne zuwa dattawa masu shekaru 65.

“ Cikin mutum miliyan biyu da aka tabbatar suna ragargazar muggan kwayoyi a Kano, an gano sun fi maskewa da kwayar Tramol ne, sai kuma kwankwaɗar Kodin da sauran magungunan tari, tabar wiwi ita ce ta karshe a jerin kwayoyin da aka fi sha a Kano.

Mu a jihar Kano ba za mu amince da kokarin halasta shan tabar Wiwi a kasar nan ba – Gargadin Ganduje

Gwamnan jihar Kano ya tabbatar wa shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa cewa jihar Kano da yan majalisar Kano ba za su biye wa masu kokarin a halasta shan wiwi a kasar nan ba.

A lokacin da yake jawabi kamar yadda Kakakin hukumar NDLEA ya sanar a wata takarda bayan ziyarar da hukumar ta kai wa gwamnan a fadar gwamnati a Kano, ya ce gwamnan ya ce babu wani zababben dan majalisa daga jihar da zai mara wa wannan kudiri baya ba.

” Kowa ya sani cewa jihar Kano ce ta fi yawan ‘yan majalisu a majalisar tarayya, za mu gaya musu kada wani ya biye wa masu son a halasta shan wiwi a kasar nan, su tabbata sun kalubalanci wannan kudiri.

Marwa ya ce kokarin da ake yi na a halasta shan wiwi a kasar nan zai maida hannun agogo baya ne na ayyuka da nasarorin da hukumar ta samu zuwa yanzu.

” Baya ga haka muna godewa gwamanatin Kano bisa goyon bayan da take baiwa hukumar sannan muna kira ga masu gidajen haya su daina baiwa yan harkallar kwayoyi gidajen su su zauna. Idan muka kama mutum zamu kwace har da gidan ta zama ta gwamnati.

” Zuwa yanzu mun kama mutum sama da 8600 kuma mun kwace kwayoyi masu nauyin kilogiram sama da miliyan 2 cikin watanni 6.

Share.

game da Author