MURNA TA KOMA CIKI: Hukumar jiragen Ƙasa ta dakatar da fara jigilar matafiya daga Legas zuwa Kano

0

Idan ba a manta ba hukumar jiragen kasa ta Kasa NRC ta sanar da fara jigilar matafiya daga Legas zuwa ta jirgin kasa daga Legas zuwa Kano daga ranar 13 ga watan Agusta.

Sai dai kuma murna ta koma ciki ranar Alhamis, awowi kafin ranar 13 da aka sanar cewa jirgin kasa zai fara tashi daga Legas zuwa Kano din.

Babban Darektan hukumar Fidelis Okiria ya sanar a wata takarda wanda Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa an dakatar da fara aikin jigilar mutane a jirgin kasan ne saboda lalacewar wasu wurare a layin dogon.

” Gobe Juma’a ya kamata jirgin kasa ya fara aiki gadan gadan amma kuma dole mu dakatar da wannan shiri na mu domin lalacewar wasu wurare a layin dogon. Ko da yake yanzu haka mun tura ma’aikatan mu su je su duba aikin sannan injiniyoyi su gaggauta gyara wuraren.

A karshe ya ce da zarar an kammala aikin za a sanar da ranar da za a fara tafiye-tafiye a wannan layin doko.

Share.

game da Author