Mun fi caɓa ciniki da dare fiye da cinikin rana a Kaduna – Inji ƴan acaban Kaduna

0

Wasu masu tuka baburan haya a Kaduna sun bayyana cewa sun fi caɓa ciniki da dare fiye da yadda suke yi da rana idan suka fito sana’a.

A tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta yi da ‘yan achaba ranar Juma’a ‘yan achaba sun ce duk da cewa sukan fuskanci matsaloli da suka hada da barayi ko ‘yan sanda amma sun fi samun ciniki da dare.

Wani dan achaba mai suna Idrisa Dankano ya ce ya fi son aikin dare, musamman a karshen mako saboda cinikin da yake samu.

” Da dare mukan ƙara farashin kuɗin hayasannan idan ka kwatanta da kudin da ake biyar da rana za ka ga an fi samu da dare.

“Muna Kara kudin ne saboda dare, nisan wuri da hadarin da za mu iya fuskanta a hanya.

Dankano ya ce duk da ƙarin farashin da suke yi da dare mutane da dama na biyan kudin a haka domin suna samun biyan bukata.

Wani dan acaban Francis Ujah ya ce da shi da kannan sa ne suke achaba da babur daya inda kannan zai yi aiki daga safe zuwa yamma sannan shi ya fara daga karfe 8 zuwa cikin dare.

“Fasinjoji dake wuraren shakatawa da club sun fi bamu hadin kai musamman idan dare ya yi.

“A dare daya na kan yi cinikin Naira 2,000 zuwa Naira 3,000 daga karfe 8 na dare zuwa 12 na dare.

“Banda matsalar haduwa da barayi da ‘yan sanda na fi son yin aiki da dare saboda yawan kudaden da nake samu.

Kabir Alhamdu, ya ce a dare daya yakan samu riban da ta fi yawan wanda yake samu da rana idan ya fita aikin dare.

“Na kan yi cinikin Naira 5,000 zuwa 7,000 a dare ɗaya musamman tsakanin karfe 8 zuwa 1 na dare.

Share.

game da Author