Fitacce kuma shahararren dan wasan kwallon kafa wanda duk duniya shine kan gaba Leo Messi ya rattaba hannu a ƙungiyar kwallon kafa ta PSG dake ƙasar Faransa.
Idan ba a manta ba, Messi da ƙungiyar kwallon kafa ta Barcelona sun yi bankwana da juna bayan ba su iya cimma matsaya ba kan kuɗin albashin da za a riƙa biyan ɗan wasan ba.
Ko da yake kungiyar da shi kansa Messi sun so ace ya ci gaba da wasa a ƙungiyar ta Barcelona amma hakan bai yiwu ba saboda wasu dokokin kasar Spain.
A ranar Talata, Messi ya dira kasar Faransa tare da iyalan sa domin karkare saka hannu a yarjejeniyar kwantaragin tsakanin sa da ƙungiyar PSG.
Discussion about this post