Matar da ta banka wa kanta wuta saboda miji zai dawo da tsohuwar matar sa a Jigawa na kwance a asibiti

0

Wata matar aure mai kimanin shekaru 25 ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi bayan ta samu labarin mijinta zai dawo da tsohuwar matarsa.

Mai magana da yawun Yan Sanda a Jigawa Lawan Adam ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa matar yar asalin garin Rungumau da ke cikin ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa yanzu haka tana kwance asibiti.

Kakakin na Yan Sanda ya bayyana cewa matar ta bulbule kanta da man fetur daga bisani ta cinna wa kanta wuta.

Bayan da ta ga uwar-bari sakamakon raɗaɗin wutar ta ke cin ta, sai ta ruga waje tana ihu tana neman taimako, inda a nan waɗanda ke kusa suka taimaka wajen kashe wutar.

Duk da dai an yi nasarar kashe wutar, amma matar ta ƙone sosai, domin kuwa kusan rabin jikinta a ƙone yake kuma tana kwance asibiti, inji Kakakin Yan Sanda na Jigawa.

Wannan lamari ya faru ne bayan makamancin hakan ya taba faruwa a Jihar Zamfara a 2019 a inda budurwa mai suna Aisha ta banka wa kanta wuta saboda saurayinta ya gaza samun kudin aurenta.

Ita dai Aisha daga baya ta rasu a asibiti lokacin da take fama da jinya.

Share.

game da Author